Iran ta ce ba za ta bar Amurka ta riƙa kai mata hari a duk lokacin da ta ga dama ba
Iran ta ce ba za ta taɓa barin Amurka ta riƙa ƙi mata hari a duk lokacin da ta ga dama ba tana mai jaddada cewa za ta mayar da martani ga duk wani hari da za a kai mata a nan gaba.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baghaei, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai, inda ya ce ƙasarsa ba za ta amince Amurka ta ƙayyade lokacin yaƙi ko zaman lafiya ba.
Ya kuma ce halin da ake ciki yanzu ba zai iya zama abin da za a kira tsagaita wuta ba.
Baghaei ya ƙara da cewa an samu ɗan sauƙin tashin hankali a cikin ‘yan kwanakin nan saboda dabarun rundunonin sojin Iran.
Ya yi gargaɗin cewa duk wani sabon mataki da Amurka ta ɗauka kan Iran zai gamu da martani mai ƙarfi daga Tehran.