Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man U na fuskantar ƙalubale kan makomar Rashford,Arsenal da Tottenham na son Nusa
Manchester United na kokarin kammala cinikin sayar da ɗan wasanta da kuma na Ingila,Marcus Rashford, mai shekara 28, kafin tawagar ƙungiyar ta tafi sansanin horaswa a Dublin a watan Agusta gabanin kakar wasa ta bana. (Sun), external
Sai dai kuma akwai shirye-shirye da aka tanada na dawo da Marcus Rashford cikin tawagar Manchester United karkashin jagorancin Michael Carrick. (Guardian), external
Arsenal and Tottenham are among five Premier League sides eyeing a move for RB Leipzig and Norway winger Antonio Nusa, 21.
Arsenal da Tottenham na cikin kungiyoyi biyar na gasar Firimiya ta Ingila da ke zawarcin ɗan wasan RB Leipzig da tawagar Norway, Antonio Nusa, mai shekara 21.(Teamtalk), external
Barcelona ta sanya ɗan wasan Faransa da Bournemouth, Eli Junior Kroupi, mai shekara 20, cikin jerin 'yan wasan da take son ɗauka. Sai dai tana iya fuskantar cikas daga Paris Saint-Germain da Arsenal da kuma Tottenham wajen samunsa (Fichajes - in Spanish), external
Juventus na son Aston Villa ta rage kuɗin da take nema domin sayar da mai tsaron ragar ƙasar Argentina, Emiliano Martinez, mai shekara 33, wanda ya kai yuro miliyan 10 , bayan ta cimma yarjejeniya da ɗan wasan kan sharuddan kwantiragi. La Gazzetta dello Sport - in Italian), external
Barcelona na goggaya da wasu kungiyoyi da dama na gasar Firimiya ta Ingila, ciki har da Chelsea da Manchester City da Manchester United, wajen zawarcin ɗan wasan Colorado Rapids da Australia, Lucas Herrington, mai shekara 18, wanda ake hasashen zai yi fice a nan gaba. (Teamtalk), external
Manchester City da Arsenal da Liverpool na cikin kungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan tsakiya na Lille , Ayyoub Bouaddi, mai shekara 18 wanda ke haskakawa tare da tawagar Morocco a gasar Kofin Duniya.(Football Insider), external
Chelsea za ta yi nazari kan yiwuwar ɗaukar ɗan wasan gaba na Juventus da Serbia, Dusan Vlahovic, mai shekara 26, idan ta yanke shawarar sake fasalin sashen 'yan wasanta masu kai hari a wannan bazarar. (CaughtOffside), external
Kocin Real Madrid, Jose Mourinho, na nazari kan yiwuwar ɗaukar ɗan wasan baya na Arsenal da tawagar Italiya, Riccardo Calafiori, mai shekara 24, da takwaransa na Arsenal, ɗan ƙasar Chile, Piero Hincapié, mai shekara 24, da kuma ɗan wasan baya na Manchester City da Portugal, Rúben Dias, mai shekara 29, yayin da yake neman ƙara ƙarfi da kuzari a bangaren masu tsaron bayan ƙungiyarsa. (Fichajes - in Spanish), external
Tsohon ɗan wasan tsakiya na Liverpool da Brazil, Fabinho, mai shekara 32, ya ce yana son sake haɗuwa da Jose Mourinho a Real Madrid bayan ya bar ƙungiyar Al-Ittihad. (Talksport), external
Sporting na shirin ɗaukar ɗan wasan gefe na Chelsea, Jesse Derry, mai shekara 19, a matsayin aro na tsawon kakar wasa guda, inda ake sa ran zai isa birnin Lisbon domin yin gwajin lafiya. (Sky Sports), external