Abubuwan da binciken ICPC ya gano kan hukumar bogi a Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa mai zaman kanta a Najeriya ICPC ta kammala bincikenta na farko kan hukumar nan ta bogi da aka gano tare da miƙa rahotonta na wucin-gadi a ranar Alhamis.

A ranar 7 ga watan jiya na Yuli ne Shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu y aba hukumar wa'adin kwanannki 30 ta gudanar da cikakken bincike game da yadda aka kafa wannan hukumar; kuma jiya ne wa'adin ya cika.

Da yake yi wa manema labarai bayani game da sakamakon binciken a fadar shugaban kasa, shugaban hukumar ta ICPC Dr. Aliyu Musa ya ce binciken ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ko wata hukumar gwamnatin ba ta nada Adeniyi Adeyemi Mathew kan wannan mukamin ba.

Haka kuma babu wata doka ko umarnin shugaban kasar da ya kafa wannan hukumar tasa.

Kazalika, takardar nadinsa kan mukamin shugaban hukumar da duk sauran takardun da hukumar tayi amfani da su wajen gudanar da ayyukkan ta suma duk na bogi ne.

Rahoton ya ce hukumar ta bogi ta tsaga majalisar ba shugaban kasa shawara kan harkokin tattalin arziki wato Presidential Economic Advisory Council inda ta samar da wasu hukumomi biyu na bogi ba bisa ƙa'ida ba.

Hukumomin su ne

  • FCT Investment Promotion Agency (FIFA)
  • Foreign Investment Promotion Agency and Public Private Partnership (FIFA-PPP).

Haka kuma rahoton ya ce ya gano cewa Adeniyi Adeyemi ya ribaci raunin da ke akwai cikin aikin tattancewa da sanya ido daga hukumomin da alhakin hakan ya rataya a wuyansu wajen tafka wannan ta'asa amma a wani matakin an samu hadin baki ko sakaci daga wasu jami'ai.

Sai dai kuma shugaban hukumar ya ce a bisa abin da binciken nasu ya gano, babu inda aka amince da bai wa hukumar kuɗaɗe daga gwamnatin tarayya kuma babu wasu kuɗaɗen da aka ba ta.

Ya kara da cewa babu wani rauni ko sakaci da suka gano a tsare-tsare ayukkan fadar shugaban kasa ko na babban bankin kasar dangane da wannan hukumar; kuma takardar Nadin Adeniyi Adeyemi ba daga fadar ta fit oba.

Rahoton ya ce domin samun saukin gudanar da hukumomin biyu da ya kirkira, Adeyemi ya kirkiri wata dokar majalisar dokoki da ta tanadi kirkirar hukumar wadda ya yi amfani da ita wajen bude asusun ajiya na hukumomin a bankuna.

An kitse rahoton bincike na wucin gadi da wasu shawarwari da suka hada da cewa a gurfanar da shi gaban sharia, sannan a dauki matakan ladabtarwa kan jami'an gwamnatin da Rashin yin aikinsu ko sakaci ya bayar da damar kafawa da gudanar da hukumar.

Daga karshe kuma a yi garambawul ga wasu cibiyoyin gwamnati.

Rahoton na hukumar ICPC dai na zuwa ne ya yin da ita kuma majalisar wakillan kasar ke ci gaba da nata bincike kan wannan badakalar.

Muhimman abubuwan da ICPC ta gano a taƙaice

PFIPC ba hukuma ba ce ta gwamnati ba

ICPC ta ce ta tabbatar da cewa ba a taɓa kafa Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC) ta kowace doka, umarnin shugaban ƙasa ko wata sahihiyar takardar gwamnati ba.

A cewar hukumar, duk da cewa PFIPC ta riƙa gabatar da kanta a matsayin hukuma ta gwamnatin tarayya, ba ta da wata kafa ta doka

Ba gwamnatin tarayya ta naɗa Adeniyi Adeyemi Mathew ba

Binciken ya nuna cewa Adeniyi Adeyemi Mathew, wanda ya riƙa bayyana kansa a matsayin Darakta Janar na PFIPC, bai taɓa samun takardar naɗi daga gwamnatin tarayya ko wata hukuma mai ikon yin hakan ba.

An yi amfani da sunan tsohuwar PEAC ba bisa ƙa'ida ba

Rahoton ya ce PFIPC ta karɓe suna, ofisoshi da wasu hanyoyin gudanar da aiki na tsohuwar Presidential Economic Advisory Council (PEAC) ba tare da izini ba domin ta ƙara samun amincewar jama'a.

An ƙirƙiri wasu hukumomi biyu na bogi

Baya ga PFIPC, ICPC ta ce Adeyemi ya ƙirƙiri wasu hukumomi biyu da ba su da wata makama ta doka:

  • FCT Investment Promotion Agency (FIFA)
  • Foreign Investment Promotion Agency and Public-Private Partnership (FIFA-PPP)

A cewar hukumar, an kuma ƙirƙiri jabun dokokin kafa waɗannan hukumomi domin buɗe musu asusun banki da gudanar da wasu ayyuka.

Ba a ba hukumar bogin kuɗin gwamnatin tarayya ba

Duk da cewa PFIPC ta riƙa gabatar da kanta a matsayin hukuma ta gwamnati, ICPC ta ce bincikenta bai gano wata hujja da ke nuna cewa gwamnatin tarayya ta ware ko ta tura mata kuɗi ba.

Mene ne mataki na gaba?

Ko da yake rahoton wucin-gadin ya amsa tambayoyi da dama, ICPC ta ce binciken bai ƙare ba.

Hukumar ta bayyana cewa tana ci gaba da binciken asusun bankunan PFIPC, na Adeniyi Adeyemi Mathew da kuma waɗanda ake zargin suna da hannu a lamarin domin gano cikakken yadda aka gudanar da ayyukan.

ICPC ta kuma ba da shawarar a gurfanar da Adeyemi a gaban kotu, tare da aiwatar da gyare-gyare a tsarin gwamnati domin ƙarfafa hanyoyin tantance sahihancin takardu da kuma hana sake faruwar irin wannan lamari a nan gaba.

Lamarin ya kuma sake jawo hankalin masana kan muhimmancin samar da ingantaccen tsarin tabbatar da sahihancin naɗe-naɗen gwamnati, dokokin kafa hukumomi da sauran takardun hukuma, domin hana masu son damfara amfani da gibin tsarin gudanarwa wajen yaudarar jama'a.

Wane ne Prince Adeniyi Adeyemi?

Kafin yanzu babu wani cikakken bayani a bayyane game da Prince Adeniyi Adeyemi, in ban da kasancewarsa shugaban hukumar PFIPC da aka fi sani da kwamitin shugaban ƙasa kan shawarwarin bunƙasa tattalin arziki..

Hukumar ta ayyana kanta a matsayin cibiyar gwamnati a shafin Instagram wadda ke "aiwatar da haɗin gwiwa don janyo masu zuba jari daga ƙetare zuwa Najeriya''.

Bisa ga bayanan shafin na Instagram, an buɗe shi ne a 2025, kuma adireshin hukumar na yanar gizo: www.pfipc.gov.ng ba ya tafiya lokacin da muke haɗa wannan labari.

To sai dai wannan Adeniyi Adeyemi ba shi ne Prince Akeem Adeniyi Adeyemi, ɗanmajalisar wakilan Najeriya ba, suna dai da suna iri ɗaya ne.

Me ƴan Najeriya ke cewa?

Ƴan Najeriya da dama sun riƙa muhawara kan batun, inda wasunsu ke bayyana batun da abin kunya ga fadar shugaban ƙasar.

Fitaccen lauyan nan na ƙasar, kuma ɗan gwagwarmaya, Femi Falana ya ce kamata ya yi Shugaba Tinubu ya kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin bincikar lamarin, musamman da batun ya haɗa da shugaban ma'aikatar fadar shugaban ƙasar.

Falana ya ce bai kamata fadar shugaban ƙasar ta ce ta wanke Gbajabiamila ko duk wani da ke da hannu a lamarin ba.

"Ya kamata fadar shugaban ƙasar ta miƙa wa hukumar ICPC ragamar binciken Gbajabiamila da sauran mutane da ke da hannu a cikin lamari, saboda a ciki akwai zarge-zargen da suka shafi damfara da cin hanci,''

"Ya kamata gwamnati ta yi wa ƴan ƙasa bayanin ta yaya aka ware wa hukumar bogi kuɗi a kasafin 2026, sannan ta yaya har ta samu asusu a Babban Bankin Ƙasar, CBN''?

Haka shi ne tsohon sanatan Kaduna Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na X cewa ya taba riƙe muƙamin mataimakin shugaban kwamitin harkokin waje na Najeriya, kuma bai taɓa ganin wata hukuma da wannan suna ba.