Dalilai 4 da suka sa aka kasa murƙushe ƴan Houthi a Yemen

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Kawo ƙarshen yaƙi da ƙungiyar Houthi da ke Yemen ya gagari kundila duk da an shafe shekaru ana kai mata hare-haren soji ƙarƙashin jagorancin ƙasar Saudiyya, wadda ta shiga yaƙin a shekarar 2015.

A cewar jaridar Business Standard ta intanet, ƙungiyar ta ci gaba da riƙe manyan yankuna masu yawan jama'a a Yemen, yayin da hare-haren sama suka kasa kawar da ita daga kan mulki.

Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen yaƙi da ƙungiyar shi ne yanayin ƙasar Yemen, wadda ke da tsaunuka masu yawa da ke ba mayaƙan Houthi damar fakewa da kuma wahalar da dakarun da ke yaƙar su.

Haka kuma, ƙungiyar na amfani da dabarun yaƙi da makaman da suka bambanta da na rundunonin soji na yau da kullum. Saɓanin ra'ayi da rarrabuwar kawuna tsakanin dakarun da ke yaƙar ta, da kuma tallafin da ake zargin tana samu daga Iran, na ƙara wahalar da yunƙurin murƙushe ta.

Bugu da ƙari, kasancewar ƙungiyar a kusa da mashigar ruwan Bab al-Mandab, wadda ke da muhimmanci wajen zirga-zirgar jiragen ruwa tsakanin Bahar Maliya da Tekun Aden, ya sa rikicin ya shafi tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.

Ga wasu dalilai da suka sa aka kasa ganin bayan ƙungiyar Houthi.

1. Tsaunuka da ke taimaka wa mayaƙan Houthi samun kariya

Mayaƙan Houthi na gudanar da ayyukansu a yankunan da ke da tsaunuka masu kwari da kuma manyan hamada, inda suke amfani da wurare masu tsayi domin ɓuya da samun galaba a fagen yaƙi.

Ɗaruruwan mayaƙan ƙungiyar sun mamaye wurare masu tsayi da ke kallon mashigar ruwan Bab al-Mandeb, wadda muhimmiyar hanyar zirga-zirgar jiragen ruwa ce da ta haɗa Bahar Maliya da Tekun Aden.

Yanayin waɗannan yankuna na kawo cikas ga yunƙurin dakarun da ke yaƙar Houthi na ci gaba da kutsawa cikin yankunan da ƙungiyar ke iko da su.

Duk da haka ana ci gaba da faɗa a yankunan hamada, ciki har da Shaab al-Jinn da ke lardin Lahj, inda dakarun da ke goyon bayan gwamnatin Yemen, tare da taimakon Saudiyya, ke fafatawa da mayaƙan Houthi.

2. Yanayin kayan yaƙi

Duk da an shafe shekaru ana kai mata hare-haren sama na soji, amma sun kasa kawar da ƙungiyar Houthi.

A shekarar 2015, kawancen ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta ya shiga yaƙin Yemen, inda ya shafe shekaru yana kai hare-hare ta sama kan mayaƙan Houthi. Duk da waɗannan hare-hare, an kasa murƙushe ƙungiyar.

Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a shekarar 2022 ta sa an samu kwanciyar hankali na wani ɗan lokaci. Sai dai tun daga lokacin, Houthi na ci gaba da kasancewa babbar barazana, tare da ci gaba da iko da yankunan da yawancin al'ummar Yemen ke zaune.

Wannan ya sa ake samun tsaiko wajen iya ƙaddamar da hare-haren sama, musamman idan ƙungiyar da ake yaƙa da ita tana ci gaba da iko da yankunan da take gudanar da ayyukanta a ƙasa, kuma tana amfani da wurare masu wahalar kai wa hari.

3. Rashin haɗin kan dakarun da ke yaƙar Houthi

Dakarun da ke yaƙar ƙungiyar Houthi ba sa ƙarƙashin rundunar soji guda mai ƙarfi ba. Ƙungiyoyin da ke goyon bayan gwamnatin Yemen sun haɗa kai ne a matsayin kawance, wanda Saudiyya ke tallafawa, yayin da wasu ƙungiyoyi masu saɓanin ra'ayi ke ƙara kawo cikas ga haɗa kai wajen gudanar da ayyukan soji.

Ana ganin wannan kawance ne "mai rauni matuƙa".

Irin wannan rarrabuwar kawuna na ƙara wahalar da daidaita hare-hare da gudanar da yaƙi cikin tsari guda a fagage daban-daban, lamarin da ke rage tasirin ƙoƙarin murƙushe mayaƙan Houthi.

4. Goyon bayan Iran na ƙara wa Houthi ƙarfi

Ƙungiyar Houthi na samun goyon bayan Iran, lamarin da ya sanya rikicin Yemen cikin babban dalilan da suka haifar da tankiya tsakanin Tehran da Saudiya, waɗanda manyan abokan hamayyar juna ne a yankin Gabas ta Tsakiya.

Wannan goyon baya na daga cikin abubuwan da ke taimaka wa ƙungiyar ci gaba da riƙe matsayinta duk da tsawon lokacin da aka shafe ana yaƙi.

Hare-haren da mayaƙan Houthi suka kai wa Saudiyya sun kuma nuna yadda rikicin zai iya shafar tsaron yankin Gabas ta Tsakiya fiye da iyakokin Yemen.

Bugu da ƙari, kasancewar mayaƙan Houthi a wuraren da ke kallon mashigar ruwan Bab al-Mandab na ƙara barazanar tsaro a yankin.

Wannan mashiga ta haɗa Tekun Maliya da Tekun Aden, kuma tana da muhimmanci wajen zirga-zirgar jiragen ruwa na kasuwanci a duniya, ciki har da jigilar man fetur zuwa ƙasashe daban-daban.

Asarar da ake tafkawa sakamakon rikicin

Rashin nasarar murƙushe mayaƙan Houthi ya tsawaita rikicin Yemen, tare da ƙara tsananta wahalhalun da fararen hula ke fuskanta.

Tun daga watan Satumba, kusan 'yan Yemen 200,000 ne suka tsere daga gidajensu, inda iyalai masu ƙaramin ƙarfi da dama ke fakewa a tsaunuka ba tare da abinci, ruwa ko barguna ba.

Asibitocin soji a birnin Aden kuma sun cika da waɗanda suka jikkata, ciki har da mutanen da suka samu raunukan harbin bindiga da kuma waɗanda aka yanke wa gaɓoɓin jikinsu.

Ma'aikatan lafiya sun ce suna kula da mayaƙan da suka jikkata daga ɓangarorin biyu ba tare da nuna bambanci ba.

Haɗuwar waɗannan dalilai na yanayin yankin da ke da wahalar shiga, nau'o'in makaman da ake amfani da su, rashin haɗin kan dakarun da ke yaƙar Houthi da kuma goyon bayan da ƙungiyar ke samu daga wajen ƙasar, na daga cikin abubuwan da suka taimaka mata ci gaba da riƙe iko duk da shafe shekaru ana matsa mata da hare-haren soji.

Tun da hare-haren sama da aka kai a baya sun kasa kawar da ƙungiyar, har yanzu ba a samu mafita da za ta aiki game da rikicin ba.