Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea na bibiyar Wijnaldum, Newcastle da Aston Villa na zawarcin Kofane
Chelsea ta tuntuɓi tsohon ɗanwasan tsakiyar Liverpool mai shekara 35, Georginio Wijnaldum, kan komawa ƙungiyar a kyauta. A bazarar bana ɗanwasan ya bar ƙungiyar Al-Ettifaq ta gasar Saudiyya. (Foot Mercato - in French)
Arsenal na nazari kan shiga zawarcin ɗanwasan gaban Faransa da Bournemouth mai shekara 20, Eli Junior Kroupi da nufin ɗaukar sa a watan Janairu. (Independent)
Mataimakin kocin Arsenal Gabriel Heinze ya tuntuɓi ɗan ƙasarsa kuma ɗanwasan gaban Inter Milan mai shekara 29, Lautaro Martinez a kan komawa taka leda a Gunners kafin rufe kasuwar ƴanwasa, amma ƙungiyar Italiyan ta ƙi amincewa da cinikin. (Mail - subscription required)
Newcastle da Aston Villa za su ci gaba da zawarcin ɗanwasan gaban Kamaru da Bayer Leverkusen mai shekara 20, Christian Kofane. (Football Insider)
Manchester United ta haƙura da neman ƴanwasan baya na gefen hagu, ƴan kwanaki kafin rufe kasuwar cinikin ƴanwasa bayan rasa samun irin ɗanwasan da ta ke fatan samu. (Express)
Everton ta ƙi amincewa da tayin £65m da Chelsea ta gabatar mata kan ɗanwasan tsakiyar Ingila mai shekara 25, James Garner, saboda ƙurewar lokaci. (Talksport)
Yanzu haka tsohon ɗanwasan gaban Manchester United da Faransa mai shekara 30, Anthony Martial, ba ya da ƙungiya kuma yana neman hanyar komawa gasar firimiya ta Ingila. (Teamtalk)
Everton ba ta da sayen ƴanwasan da basu da ƙungiya a yanzu haka, masu ƴancin ƙulla yarjejeniya da ƙungiyoyi saboda babu wata kwangila a kansu. (Telegraph - subscription required)
Ɗanwasan gaban Brazil da Tottenham mai shekara 29, Richarlison, ya amince zai koma ƙungiyar Turkiyya, Trabzonspor inda ake sa ran za a riƙa biyan sa albashin da ya ninka wanda Spurs ke biyan sa har sau uku. (Fabrizio Romano)
Chelsea za ta fafata da Liverpool wajen zawarcin ɗanwasan tsakiyar Monaco, Lamine Camara mai shekara 22. (Talksport)