Manyan ɗariku 5 da Kiristocin Najeriya suka fi bi

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Kamar yadda yake a kowane addinin akan samu bambance-bambance tsakanin mabiya addinin.

Akan samu wannan bambanci ne daga aƙida ko hanyar ibada da kuam tsarin jagoranci.

Akwai manyan ɗariƙun Addinin Kirista a duniya da suka shahara tsakanin mabiya addinin.

Najeriya na daga cikin ƙasashen da suka fi yawan Kiristoci a nahiyar Afirka, kuma suke bin bambantan ɗariƙun addinin.

Rev. Jonh Joseph Hayaf, shugaban Ƙungiyar Kiristocin Najeriya reshen arewacin ƙasar ya bayyana wa BBC wasu daga cikin manyan ɗariƙun da Kiristocin Najeriya suka fi binsu.

Kotolika

Dariƙar Katoli na ɗaya daga cikin manyan ɗariƙun Addinin Kirista a duniya, kuma yana daga cikin ɗariƙun da suka fi shahara tsakanin Kiristocin Najeriya.

Rev. Jonh Joseph Hayaf ya ce ɗariƙar Katolika na daga cikin ɗarikun da suka fi jimawa a Najeriya.

''Dariƙar Katolika na nan a kowane yanki a Najeriya, saboda shahararsa ana iya cewa babu yankin da babu ɗariƙar a Najeriya'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Kodayake ɗariƙar na kowane ɓangare na Najeriya, amma Rev. Jonh Joseph Hayaf ya ce ta fi ƙarfi a yankin kudu maso gabashin ƙasar.

Masanin addinin Kiristan ya ce babban abin da ɗariƙar Katolika ta bambanta da sauran ɗariƙu shi ne tsarin shugabancinta.

''Ita ɗariƙar Katolika tana da shugaba guda ɗaya na duniya, da ake kira Fafaroma, kuma su shugabanin ba su aure, saɓanin sauran ɗariƙu'', in ji shi.

Angalican

Ɗariƙar Angalican, wadda ta samo asali daga Ingila ta kasance kan gaba a yawan mabiya a Najeriya.

Rev. Jonh Joseph Hayaf ya ce kusan a kowane ɓangare na Najeriya ana samun ɗariƙar Anglican, kodayke ya ce ta fi yawan mabiya a yankin Kudu maso gabashin ƙasar.

''Ya kuma ce hakan ba ya rasa nasaba da yadda Turawan mulkin mallaka na da ƴan mishan suka fara shigo Najeriya ta yankin'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Rev. Jonh Joseph Hayaf ya ce a tsarin ɗariƙar Angalican sukan yi amfani da shugabanni na Bishop-Bishop na ƙasashe daban-daban.

Sannan kuma su shugabanninsu kan yi aure, saɓanin na ɗariƙar Katolika.

Bapdist

Ikilisiyyar Baptist na cikin ɗariƙun Addinin Kirista da suka fi yawan mabiya a Najeriya.

Rev. Jonh Joseph Hayaf ya ce ɗariƙar Baptist ta fi ƙarfi a yankin kudu maso yammacin Najeriya da wasu yankunan arewacin ƙasar, kuma ana samun wannan ɗariƙa kusan a kowane ƙauye na yankunan Arewa ta Tsakiyar Ƙasar.

Ya ƙara da cewa ɗariƙar Baptsit ta yarda da tsarin dimokraɗiyya a cikin shugabancinsu.

''Dangane da Bapdistma (wankan tsarki) akan yi wa mutumin da ya balaga ne'', in ji shi.

Sannan ya ce a ɗariƙar Baptist kowane Coci shugabancinta na ƙarƙashin Fartonta.

Ya ƙara da cewa kowace coci, ita ce ke da alhakin tara kuɗinta, sannan ta biya fastonta.

Methodist

Idan ana maganar ɗariƙun Addinin Kirista da suka fi yawan mabiya a Najeriya ba za a manta da ɗariƙar Methodist ba.

Shugaban ƙungiyar Kiristocin Najeriya reshen arewacin ƙasar, ya ce wannan ɗariƙa galibi ta fi rinjaye a kudancin ƙasar, kodayake ya ce aka samu mabiyanta a wasu sassan arewaci.

''A yankin arewacin Najeriya, wannan ɗariƙa ta fi ƙarfi a jihar Benue, kodayake tana da rinjaye a wasu yankunan kudancin ƙasar'', in ji Rev. Jonh Joseph Hayaf.

Masanin Addinin Kiristan ya ce a tsarin Methodist akan yi wa mutum Baptistma ne tun yana jariri, saɓanin ɗariƙar Baptist da take yi wa mutum idan ya balaga.

Haka ma dangane da tsarin shugabanci, a ɗariƙar Methodist shugabancin coci na ƙarƙashin Bishop na yankin da cocin take.

''A wannan ɗariƙa kuɗaɗen da ake tarawa a yanki ne ake amfani da su wajen biyan fastocin cocin'', in ji shi.

Ecwa

Ecwa ta kasancewa ɗaya cikin ɗariƙun Addinin Kirista masu yawan mabiya a Najeriya.

Rev. Jonh Joseph Hayaf ya ce ɗariƙar ta fi ƙarfi yankin arewa ta tsariyar ƙasar.

''Abin da ya kama daga Zungeru da Abuja da Jos da wasu yankunan Bauchi da Gombe'', kamar yadda ya bayyana.

Me ya sa Kiristocin Najeriya ke bin waɗannan ɗariƙu?

Rev. Jonh Joseph Hayaf ya akwai dalilai masu yawa da suka Kiristocin Najeriya ke bin waɗannan ɗariƙu.

Masanin Addinin Kiristan ya alaƙanta zuwan Turawan mulkin mallaka na ƴan Mishan da yin tasiri ga yaɗuwar waɗannan ɗariƙu tsakanin Kiristocin ƙasar.

"Tarihi ya nuna cewa Turawan Mishan da na mulkin mallaka sun yi aiki tare, kuma duk inda suka je suna kafa coci, kuma Turawan da suka yi wa Najeriya Mulkin Mallaka ƴan Ingila ne, kuma Cocin Ingila ƴan Angalican ne, don haka ne ma dun inda Turawan mulkin mallaka suka zauna'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Rev. Jonh Joseph Hayaf ya ci gaba da cewa ɗariƙar Katolika kuma ta yi tasiri a Najeriya ne tun lokacin da ƴan misan ɗinsu suka fara zuwa ƙasar a farko-farkon kafuwar ƙasar.

Ya ce irin busharar da wakilan ɗariƙar suka yi da dabarar da suka bi wajen yaɗa busharar ta taimaka wajen sama wa ɗariƙar mabiya a Najeriya.

''A lokacin sauran ɗariƙun Kirista idan mutanensu sun yi karatu sukan so mutanen su zo su yi aiki a ɗariƙunsu, amma su ɗariƙar Katolita, idan nasu ya yi karatu sukan so ya yi aiki a gwamnati''.

''Wannan ya taimaka wajen baza ɗariƙar Katolika ta hannun gwamnati zuwa kowane ɓangare na ƙasar'', kamar yadda ya bayyana.

Masanin Addinin Kiristan ya ce wani abu da ya ƙara sa waɗannan ɗariuƙu suka samu tarin mabiya a Najeriya shi ne hanyar gudanar da ibadunsu.

"Galibi mutanen Afirka, suka riƙe al'ada da muhimmanci, su kuma waɗannan ɗariƙu ba su zo da wasu abubuwan da suka saɓa wa al'adun ƴan Najeriyar ba'', in ji shi.

Ya ce mutanen Najeriyar sun fahimci cewa wasu daga cikin hanyoyin gudanar da rayuwarsu ya yi daidai da koyarwar waɗannan ɗariƙu.

Rev. Jonh Joseph Hayaf ya ce wani ƙartin dalilin shi ne da waɗannan ɗariƙu suka shigo Najeriya, sun yi ƙoƙarin ilimantar da ƴanƙasar ilimin ɗariƙun sannan aka sanya su cikin masu bushara kuma da harsunan da suke ji.

''Duk waɗanda aka je wa da bushara ba su buƙatar sai an fassara musu kafin su san saƙon da ake ɗauke da su, duk abin da aka faɗa sun gane'', in ji shi.