Iran ta yi tir da barazanar Isra'ila kan jagoranta Khamenei
Jakadan Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya, Amir Saeed Iravani, ya yi Allah wadai da barazanar da Isra'ila ta yi wa jagoran ƙasar Mojtaba Khamenei.
Ya aika wasiƙa ga babban sakataren MD da kuma shugaban kwamitin tsaro na majalisar.
A cikin wasiƙar, Iravani ya bayyana kalaman ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz, kan Mojtaba Khamenei a matsayin "ta'addancin" da kuma "keta kundin tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya."
Ya ce furucin da Katz ya yi cewa Mojtaba Khamenei "yana cikin waɗanda aka sa a layin mutanen da za a kashe" na daga cikin manufar Isra'ila ta kashe manyan jami'an Iran.
Ya yi mai zargin cewa shiru da kwamitin tsaron MDD ya yi ne ya ƙara wa Isra'ila ƙarfin gwiwar ci gaba da irin abubuwan da take yi.
Shi ma ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya ce duk wata barazana ga al'ummar Iran ko shugabanninta za ta fuskanci "martani cikin gaggawa kuma mai ƙarfi."