Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 23 ga watan Yunin 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Akwai hujjojin da ke nuna Isra'ila ta aikata laifuffukan yaƙi a Gaza - Rahoto

    Wani kwamitin bincike na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya zargi Isra'ila da kai hare-hare kan yara Falasɗinawa da gangan, lamarin da kwamitin ya ce aikata kisan kiyashi ne da laifuffukan yaƙi a Gaza da cin zarafin bil'adama a Yamma Kogin Jordan.

    A cikin sabon rahoton, kwamitin ya yi zargin cewa da gangan hukumomin Isra'ila da jami'an tsaronta suka "aikata ayyukan da suka jawo mutuwa da kuma mummunar illa ga lafiyar dubban yara Falasɗinawa," kuma an ci gaba da kashe-kashen duk da cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Oktobar 2025.

    Kwamitin ya ce yana da ƙwararan hujjojin da suka ayyana waɗannan abubuwan da Isra'ila ta yi a matsayin "wata dabara ta lalata makomar Falasɗinawa a Gaza ta hanyar kai hari kan yaransu."

  2. Ƴansanda ba za su gudanar da sahihin bincike kan kisan Ummulkhair ba - Amnesty

    Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta buƙaci hukumomin Najeriya su kafa kwamitin bincike na musamman domin binciken kisan Ummulkhair, wata malamar Islamiyya da jama'a suka yi wa kisan gayya a Maraban Jos na jihar Kaduna.

    A wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta ce ba ta da yaƙinin cewa rundunar ƴansandan Najeriya za ta gudanar da bincike na gaskiya kan lamarin.

    Amnesty ta ce an sha yin irin waɗannan alƙawura na gudanar da bincike a baya, amma sai a watsar da batun ba tare da an samar da adalci ga waɗanda abin ya shafa ba.

    "Ikirarin da ƴansanda suka yi na cewa sun fara bincike ba ya da wani tasiri, domin an yi irin waɗannan alkawuran a baya kuma ba su samar da adalci ga waɗanda aka zalunta ba," in ji Amnesty.

    Ƙungiyar ta kuma ce zarge-zargen da ake yi wa babban jami'an ƴansanda na yankin DPO, da hannu a abin da ya faru ya sa suke shakku kan yiwuwar gudanar da bincike na gaskiya.

    Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna dai ta ce ta gurfanar da mutum 24 a gaban kotun majistare bisa zarginsu da hannu a kisan wata matar aure da wasu fusatattun mutane suka yi a Maraban Jos.

  3. MDD ta ce ana amfani da fyaɗe a matsayin makamin yaƙi a Sudan

    Wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar ya gano cewa ana amfani da cin zarafin mata ta hanyar fyade a matsayin makamin yaƙi a Sudan.

    Babban jami'in kare haƙƙin bil adama na Majalisar Ɗinkin Duniya Volker Türk, ya ce wasu daga cikin hare-haren na da nasaba da ramuwar gayya bisa zargin goyon bayan ɓangarori daban-daban na rikicin, yayin da wasu kuma ke da alaƙa da bambancin ƙabila.

    Volker Türk ya yi gargaɗin cewa wasu daga cikin waɗannan hare-haren na iya zama laifukan cin zarafin bil'adama.

    Ofishinsa ya tabbatar da aukuwar fiye da irin waɗannan hare-hare 500 tun bayan fara yaƙin basasar Sudan shekaru huɗu da suka gabata.

    Yawancin laifukan dai ana zargin mayaƙan rundunar RSF da sojojin Sudan da ƙawayensu da kuma wasu ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ne da aikata su.

    Mafi akasarin waɗanda abin ya shafa sun kasance mata ne da 'yan mata.

  4. Amurka ta gano wani ɗan Najeriya cikin masu ɗaukar nauyin ISIS a Afrika

    Gwamnatin Amurka ta sanya sunan wani ɗan Najeriya mazaunin Legas, Muhammad Mukhtar Adamu, cikin jerin mutanen da take zargi da taimaka wa ƙungiyar ISIS a Afrika ta Yamma.

    Ta ce yana amfani da kamfanoninsa na canjin kuɗi wajen tura kuɗaɗe ga ƙungiyar.

    A wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar ranar Litinin, mai magana da yawunta, Thomas Pigott, ya ce zargin ya shafi mutum uku da kamfanoni shida da ake zargi da taimaka wa ƙungiyar ISIS wajen gudanar da harkokin kuɗaɗenta a sassa daban-daban na duniya.

    Daga cikin kamfanonin shida, uku na Najeriya ne, inda biyu ke jihar Legas yayin da ɗaya ke jihar Kano.

    Kamfanonin sun haɗa da Nine To Nine Exchange Bureau De Change Limited da ke harabar filin jirgin sama na Legas, da Manhattan Bureau De Change Limited da ke titin Murtala Mohammed a Kano, da kuma Generation Currency Bureau De Change Limited da ke Legas.

    Amurka ta kuma sanya takunkumi kan kamfanonin canjin kuɗin guda uku da ta ce Adamu ne ke mallaka ko kuma yake sarrafa su.

    Hukumar Kula da Kadarorin Ƙetare ta Amurka (OFAC) ta Sanarwar ta ce mutanen da kamfanonin da aka aka gano sun fito ne daga ƙasasheirinsu Faransa, Syria, Turkiya da Najeriya.

    Bayanin ya ce Adamu na zaune ne a gida mai lamba 45, da ke titin Abimbola, kusa da Capital Road, ta yankin Agege a jihar Legas.

    Ta kuma ce an haife shi a Najeriya a ranar 2 ga Agustan 1990, amma kuma wasu bayanai sun nuna ranar 3 ga Agustan shekarar.

    Sauran mutanen biyu da aka sanya wa takunkumin su ne Abderrahmane Miloud, wanda aka fi sani da Ghazi Ibrahim, ɗan ƙasar Faransa da ake zargi da gudanar da mu'amaloli da mutanen da ke da alaƙa da ISIS tare da bayar da bayanai kan abubuwan fashewa ga magoya bayan ƙungiyar.

    Na uku kuwa shi ne Abdelhakim Boukich, wanda aka fi sani da Babili Muhammad, wanda Amurka ta bayyana a matsayin mai taimaka wa masu tsattsauran ra'ayi da kuɗi daga ƙasar Siriya, kuma tana zarginsa da sarrafa wata manhajar musayar kuɗin Bitcoin da ake amfani da ita wajen mu'amalolin da ke da alaƙa da ISIS.

  5. Nijar ta fice daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya

    Gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar ta miƙa buƙatarta ta ficewa daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya, ICCC, a hukumance.

    Wannan na zuwa ne watanni tara bayan sanar da aniyarta ta barin kotun.

    Nijar ta sanar da aniyarta ta ficewa daga kotun a watan Satumban bara tare da ƙasashen Mali da Burkina Faso.

    Kotun mai hedikwata a birnin Hague ta ce ta karɓi buƙatar ficewar Nijar daga cikinta a hukumance a ranar 18 ga watan Yuni, 2026, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

    ICC ta ce ficewar ƙasar ba za ta fara aiki nan take ba, domin dokokin kotun sun tanadi cewa sai bayan shekara guda da miƙa sanarwar ficewar za ta tabbata.

    Kotun ta kuma jaddada cewa har zuwa lokacin da ficewar za ta fara aiki, Nijar za ta ci gaba da cika dukkan ƙa'idojin da suka wajaba a kanta a matsayinta ta mamba.

    Dukkanin ƙasashen uku na yankin Sahel na ƙarƙashin gwamnatocin soji ne da suka karɓi mulki ta hanyar juyin mulki tsakanin shekarun 2020 da 2023.

    Gwamnatocin ƙasashen sun zargi kotun da abin da suka kira salon mulkin mallaka, inda suka ce tana nuna son kai ga ƙasashen Afirka.

    Babbar ƙawar ƙasashen uku, wato Russia, ita ma ba ta amince da ikon kotun ba.

  6. Sojojin Isra'ila sun buɗe wuta kan wasu mutane a Lebanon

    Kafofin watsa labarai na Lebanon sun ce mutum biyu sun rasu bayan sojojin Isra'ila sun buɗe wuta a kusa da wata mota ƙirar Buldoza da ke aikin gyaran hanya a garin Nabatiyeh da ke kudancin ƙasar.

    Lamarin na zuwa ne bayan kwanaki uku da tsagaita wutar ya ci gaba da aiki ba tare da rahoton kashe-kashe ba a karon farko tun watan Afrilu, lokacin da aka fara yunƙurin samar da dawwamammen tsagaita wuta.

    A cikin wata sanarwa, sojojin Isra'ila suka fitar, sun ce sun kai hari kan "'yan ta'adda masu ɗauke da makamai da suka kasance barazana kai tsaye" ga dakarunsu, sai dai ba a bayyana ko suna magana ne kan wannan hari ba.

    A gefe guda kuma, ƙungiyar Hezbollah ta zargi Isra'ila da keta yarjejeniyar tsagaita wutar a fili.

  7. Birtaniya za ta rufe wasu makarantu saboda tsananin zafi

    An shirin frufe bangarorin wasu makarantu a Birtaniya saboda yanayin tsananin zafi.

    Yanayin zafi a sassan yankunan Devon da Cornwall na iya kai wa sama da 30C kuma Hukumar Tsaron Lafiya ta Burtaniya (UKHSA) ta ba da sanarwar samun matsananci zafi a yankin Kudu maso Yamma.

    Sakamakon hauhawar yanayin zafi, yawancin makarantu a faɗin Devon da Cornwall da Tsibirin Channel suna rufe wasu ɓangarorinsu, ko shirin rufewa daga baya a cikin mako, ko barin iyaye su yanke shawarar kawo yayansu ko kuma barin su a gida.

  8. Tinubu ya aika wa Majalisar Dattawa ƙudirin kafa ƴan sandan jihohi a Najeriya

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya aika wa Majalisar Dattawa ƙudirin dokar gyaran kundin tsarin mulki da ke neman kafa ƴan sandan jihohi.

    Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya sanar da hakan a zaman majalisar na ranar Talata, inda ya ce sanatocin za su fara duba ƙudirin a ranar Laraba.

    Akpabio ya kuma bayyana cewa su ma gwamnatocin jihohi su yi nazarin ƙudirin.

    Ƙudirin dokar na neman a yi gyare-gyare ga wasu sassan kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 domin samar da tsarin doka da zai ba da damar kafa rundunar ƴan sandan jihohi a faɗin ƙasar.

  9. Ministan Kenya ya dakatar da gina cibiyar killace masu cutar Ebola da Amurka ke tallafa wa

    Ministan lafiya na Kenya Aden Duale ya dakatar da aikin gina wata cibiyar keɓe masu fama da cutar Ebola da Amurka ke yi a ƙasar kwana guda bayan da aka same shi da wulaƙanta kotu saboda yin watsi da hukuncin da alƙali ya yanke.

    Da ya bayyana a gaban kotu a ranar Talata, Duale ya nemi afuwa, ya kuma ce ya ba da umarnin dakatar da aikin ginin a wani sansanin soji da ke garin Nanyuki nan take.

    A watan da ya gabata ne dai babbar kotun ta yanke hukuncin dakatar da gina cibiyar killace mutane mai gadaje 50 har sai an saurari ƙarar da wata ƙungiyar kare hakkin bil-Adama ta shigar.

    Amma a ranar litinin alƙali ya yanke hukuncin cewa Duale ya yi watsi da wannan umarni kuma ya bar aikin ya ci gaba.

    An yi tanadin wurin ne domin keɓe ƴan ƙasar Amurka da ake zargin sun kamu da cutar Ebola wanda a halin yanzu da ake fama da ita a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.

  10. An gurfanar da mutum 24 bisa zargin kisan matar aure a Maraban Jos

    Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta gurfanar da mutum 24 a gaban kotun majistare bisa zarginsu da hannu a kisan wata matar aure da wasu fusatattun mutane suka yi a Maraban Jos.

    Ana tuhumar waɗanda ake zargin da laifukan bayar da gudummuwa wajen aikata laifi, tayar da hankalin jama'a, lalata dukiyoyi, lalata kadarorin gwamnati da na 'yan sanda, da kuma kisan kai.

    Wata sanarwa da kakakin rundunar ta jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya fitar ta ce an gurfanar da su ne bayan binciken da 'yan sanda suka gudanar kan lamarin da ya faru a ranar 21 ga Yunin 2026, lokacin da aka kashe matar "bayan mutanen sun ƙwace ta daga hannun 'yan sanda."

    An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 21 ga Yulin 2026, inda kotun ta bayar da umarnin a tsare dukkan waɗanda ake zargin a gidan yari har sai an kammala shari'ar.

    Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ƙara da cewa har yanzu ana ci gaba da binciken fiye da mutum 100 da ake zargin su da hannu a lamarin, tare da alƙawarin gurfanar da duk wanda bincike ya nuna yana da laifi.

  11. NAHCON ta kammala jigilar Alhazan Najeriya

    Hukumar alhazai ta Najeriya NAHCON ta ce a hukumance ta kammala jigilar alhazan Najeriya sama da 38,000 da suka tafi ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2026.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar NAHCON, Hajiya Fatimah Usara ta fitar ta ce ana sa ran jirgin ƙarshe ɗauke da alhazai daga Jihar Zamfara zai iso Najeriya a ranar Talata.

    Usara ta ce kammala jigilar ya kawo ƙarshen ayyukan Hajjin 2026.

    Sai dai ta ce alhazan Najeriya 12 a halin yanzu suna jinya a asibitoci daban-daban na ƙasar Saudiyya saboda wasu matsalolin lafiya.

    “NAHCON na bin diddigin halin da suke ciki, kuma ta shirya yadda za a dawo da su Najeriya lafiya da zarar an sallame su daga asibitoci.'' in ji ta

    Usara ta ce, an ɗauki darassa masu ma’ana daga wannan aikin Hajjin bana, wanda za a yi amfani da su wajen inganta ayyukan Hajji da za su biyo baya.

    Ta ce a bisa ƙudirin hukumar na ci gaba da inganta ayyukanta da kuma fara shiri tun da wuri, ta fara shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2027 a hukumance.

  12. Trump na sa ran kyakkyawar dangantaka da Colombia a ƙarƙashin sabon shugaba

    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi hasashen samun "dangantaka mai aminci" tsakanin gwamnatinsa da Colombia bayan sakamakon farko na zaɓen da aka gudanar ya nuna cewa ɗan takarar mai ra'ayin mazan jiya Abelardo de la Espriella ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar Lahadi.

    Ƙidayar kuri’u na farko ya nuna de la Espriella ya doke abokin hamayyarsa, Iván Cepeda, da wani ratan da bai kai kashi ɗaya cikin 100 ba.

    Har yanzu Cepeda bai amince da sakamakon ba, yana mai cewa zai jira a tantance sakamakon tukunna, wanda ya kan ɗauki kwanaki da dama.

    Trump dai ya goyi bayan de la Espriella gabanin zaɓen zagaye na biyu kuma ya bayana Cepeda a matsayin "Mai tsattsaurar ra'ayi".

    Da yake magana da manema labarai a ranar Litinin, Trump ya ce de la Espriella “ya yi nasara cikin sauki”, duk da cewa nasarar da ya samu na kashi 0.96 cikin 100 a ƙidayar farko ita ce mafi ƙanƙanta a tarihin Colombia.

  13. Gwamnati za ta ci gaba da gudana yayin da Starmer ya ke Firaminista - Downing Street

    Gwamnatin Birtaniya ta sanar da cewa ba za a ɓullo da wasu sabbin "manyan manufofi" ko yanke shawarar kashe kuɗi ba yayin da ake shirin mika mulki ga sabon Firaminista.

    Keir Starmer ya faɗawa taron majalisar ministoci da safiyar yau cewa yana son miƙa mulki cikin tsari kuma zai ba da cikakken goyon bayansa ga magajinsa.

    Shugaban ma’aikata na ƙasar ya rubutawa shugabannin ma’aikatun gwamnati cewa su bi tsarin da aka kafa na sauya firaminista.

    "Firaministan ya amince da cewa ba za a ɓullo da wata sabuwar manufa ko shirin kashe kudi da za a fara a wannan lokacin ba," in ji mai magana da yawunsa.

    Amma - mafi mahimmanci - wannan bai nuna ya haɗa da shirin zuba jari na tsaro da aka jinkirta ba, wanda ministocin suka nace cewa za a wallafa shi kafin taron Nato a ranar 7 ga Yuli.

    Da aka tambaye shi ko haramcin sabbin sanarwar manufofin yana nufin gwamnati ta fuskanci dakatarwa, kakakin ya ce ministocin suna nan a kan kujerunsu kuma "ayyukan gwamnati na ci gaba da gudana".

  14. Dole ne Iran ta kashe kuɗin da za mu sakar mata a cikin Amurka - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya sake nanata cewa duk wani kuɗin Iran da aka riƙe, wanda za a saki sanadiyyar ɗage takunkumai da gwamnatin Amurka ta yi, za a tura kuɗin ne zuwa cikin wani asusu na musamman wanda ke ƙarƙashin kulawar Amurkar.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta, Mista Trump ya ce daga cikin asusun ne Iran za ta iya amfani da kuɗin wajen sayen abinci da magunguna, kuma daga Amurka kawai za ta saya.

    A baya Iran ta yi watsi da sharuɗɗa makamantan haka daga mataimakin shugaban Amurka J.D Vance wanda ya jagoranci tattaunawar sasanci da Iran a ƙasar Switzerland.

    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya a birnin Geneva ya ce Iran ce kadai take da ƴancin tantance yadda za ta yi, da kuma abin da za ta yi da kadarorinta da za a saki.

  15. Tallafin cutar HIV da Amurka ta cire a Afirka ta Kudu na iya janyo asarar rayuka - MDD

    Shugaban hukumar kula da cutar HIV ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargaɗin cewa matakin da Amurka ta ɗauka na janye ɗaukacin tallafin da take bayarwa kan cutar HIV a Afirka ta Kudu na iya haifar da asarar rayuka.

    Shugabar UNAids Winnie Byanyima ta shaida wa manema labarai gabanin taron Majalisar Dinkin Duniya kan cutar, cewa matakin na Amurka na iya jefa waɗanda ke ɗuek da cutar cikin mawuyacin hali.

    Afirka ta Kudu ba ta dogara kan tallafin da Amurka ke ba wa ta fannin magungunan cutar ba, amma Amurka ta ba da gudummawa sosai ga shirye-shiryen ƙasar na hana yaɗuwarta.

    Jami'an Amurka sun shaida wa BBC cewa rage tallafin wani ɓangare ne martanin Amurka kan rashin kare rayukan al'ummar farar fata da ake zargin gwamnatin Afirka ta Kudu ta gaza.

    Zargi da Pretoria ta musanta.

    Ma'aikatar lafiya ta Afirka ta Kudu ta mayar da martani da cewa duk da cewa ba a sanar da ita wannan matakin a hukumance ba, amma ta daɗe tana aiki kan shirin dogaro da kai.

  16. Shugaban Iran Masoud Pezhkian ya isa Pakistan domin ziyarar diflomasiyya

    Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezhkian, ya isa Pakistan domin wata ziyarar kwana ɗaya, inda zai gana da manyan shugabannin ƙasar.

    Bayan isarsa, ya gana da firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, a cikin ci gaba da tattaunawar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

    Haka kuma, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya isa Pakistan domin haɗuwa da shugaban ƙasar a wannan ziyara, bayan ya fito daga Oman inda ya je tattaunawa kan yadda za a tafiyar da mashigar Hormuz.

    Araqchi ya je Oman ne daga Switzerland, inda ya halarci tattaunawar sulhu da aka yi tsakanin Iran da Amurka, tare da wata tawagar Iran da ta haɗa da kakakin majalisar dokoki Mohammad Baqer Qalibaf.

    Kafin isowar shugaban ƙasar Iran, Araqchi ya gana da Shugaban Pakistan da firaminista a Islamabad a wani ɓangare na shirye-shiryen ziyarar.

  17. Ba ma da shirin bai wa IAEA damar binciken tashoshinmu na nukiliya – Iran

    Iran ta ce ba ta da wani shiri a halin yanzu na bai wa Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) damar binciken cibiyoyinta na nukiliya da suka lalace sakamakon yaƙi.

    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai, inda ya ce babu wata yarjejeniya da ta tanadi irin wannan batu.

    Ya ce Iran za ta ci gaba da bin tsarin da take amfani da shi a yanzu a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT) da kuma dokokin kulawa da makaman nukiliya.

    “Gaba ɗaya babu wata doka ko tsari a kan wannan batun. A matsayinmu na mamba a yarjejeniyar NPT, za mu ci gaba da bin hanyoyin da muke kai yanzu, kuma tsarin a bayyane yake,” in ji Baghaei.

    Hakazalika, ya ce babu wata ganawa da aka shirya tsakaninsa da babban daraktan IAEA, Rafael Grossi, a Switzerland.

    Wannan bayani na Iran ya zo ne bayan kalaman Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, wanda ya bayyana cewa Iran ta amince a ba masu binciken damar bincikar cibiyoyin nukiliyarta.

    Sai dai gwamnatin Iran ta musanta wannan ikirari, tana mai cewa ba ta ɗauki wani sabon alƙawari dangane da batun binciken nukiliya ba, kuma hulɗarta da IAEA za ta ci gaba ne a ƙarƙashin dokokin da ake da su.

  18. Wani abun fashewa ya tashi a wata kasuwa dake Lagos

    Wani abun fashewa ya tashi a wani sashe na kasuwar Mushin da ke Lagos a ranar Litinin, inda mutum guda ya jikkata bayan wata mota ta tarwatse sakamakon fashewar.

    Lamarin ya faru ne da tsakar dare a wani wuri da ke 22, Oke Mushin, inda aka ajiye motar a cikin kasuwar kayan takalma.

    Mazauna yankin sun bayyana cewa ana zargin wani ne ya dasa abun fashewa (IED) a ƙarƙashin motar da ta tarwatse, amma har yanzu ba a gano mamallakin motar ba.

    Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Fatai Tijani, ya ce sun samu rahoton fashewar, kuma nan take suka tura ƙwararrun jami’an kwance abubuwan fashewa (EOD) zuwa wurin.

    Ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa an sanya IED ɗin ne a ƙarƙashin motar a ɓangaren fasinja, kuma ya fashe ne a lokacin da aka kunna injin motar.

  19. Qalibaf da Araqchi sun tafi Oman kan batun Mashigar Hormuz

    Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, tare da babban mai shiga tsakani Abbas Araqchi, sun tafi ƙasar Oman domin tattaunawa kan yadda za a tafiyar da Mashigar Hormuz.

    Rahotanni sun ce Qalibaf ya bar Tehran zuwa Muscat jim kadan bayan dawowarsa daga tattaunawar Iran da Amurka da aka yi a Switzerland, inda batun sarrafa mashigar ya zama muhimmin abu.

    Ana sa ran tawagar Iran za ta gana da Sarkin Oman, Haitham bin Tariq, domin tattauna shirye-shiryen Iran kan kula da mashigar da kuma karfafa hadin gwiwar ƙasashen biyu.

    Wannan na zuwa ne bayan kammala zagayen farko na tattaunawar Iran da Amurka, wanda ya sa tawagar Iran komawa gida kafin sake wasu muhimman ganawa.

    A wani ɓangare kuma, fadar shugaban Iran Masoud Pezeshkian ta sanar da cewa zai kai ziyara Pakistan na kwana guda, domin gode wa kokarin sasanci da kasar ta yi tsakanin Iran da Amurka tare da bunƙasa hulɗar tattalin arziki.

  20. Sojojin Najeriya sun ce sun kuɓutar da mutane 47 daga hannun ISWAP a Borno

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Hadin Kai a yankin Arewa maso Gabas ta ceto mutum 47, yawancinsu mata da ƙananan yara, da mayaƙan ISWAP suka tsare a yankin Kangarwa da ke ƙaramar hukumar Kukawa a jihar Borno.

    A cikin sanarwar da rundunar ta fitar, ta bayyana cewa an samu nasarar ceto mutanen ne a ranar 20 ga watan Yuni 2026, bayan wani gagarumin samame da sojojinta suka kai wanda ya tilasta ‘yan ta’addar tserewa suka bar waɗanda suka sace.

    Ya ce hare-haren kasa da na sama da dakarun suka kai wa sansanonin ISWAP a yankin Tafkin Chadi ne ya sa ‘yan ta’addar suka rikice suka bar wuraren da suke, lamarin da ya bai wa wadanda aka tsare damar tsira bayan dogon lokaci a hannunsu.

    A yanzu haka, an kai waɗanda aka ceto wuraren tsaro inda ake basu kulawar lafiya da taimakon jin kai, yayin da rundunar ta sake jaddada ƙudurinta na ci gaba da kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci da dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.