Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 19/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 19/10/2026

Rahoto kai-tsaye

Rabi'atu Kabir Runka

  1. Tattalin arzikin China ya haɓaka

    Tattalin arzikin China ya haɓaka, inda ya ƙaru da kashi hudu da rabi cikin ɗari a rubu'i na uku na wannan shekarar.

    Farfaɗowar ta samo asali ne sakamakon karuwar bukatar da ake da ita ta na'urorin kwamfuta da sauran kayan aikin da ake amfani da su wajen gina cibiyoyin tattara bayanai na fasahar (AI).

    Masu sharhi sun ce kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje na rufe giɓin da ake samu daga raguwar kuɗaɗen da ake kashewa a cikin gida.

    Wakiliyar BBC ta ce a cikin gida, mutanen China ba sa son kashe kuɗi yayin da Gwamnatocin ƙananan hukumomi ke fama da manyan basussuka, kuma rashin aikin yi ke kara yawa tsakanin matasa.

  2. Macron ya fara ziyarar ƙasashen gulf kan batun makamashi

    Shugaba Emmanuel Macron ya fara wata ziyara a ƙasar Kuwait yayin da gwamnatin Faransa ke ci gaba da ƙoƙarin shawo kan matsalar mummunar zanga-zanag da faru a ƙarshen makon nan.

    Har jiya Lahadi ba a tabbatar da cewa shugaban Faransa zai yi wannan tafiya ba, duk sai dai ya yi wasu kalamai da yammacin jiya Lahadi da suka nuna alamun zai yi tafiyar.

    Ya ce, "Na ɗauki matakai da dama a matakin ƙasa da ƙasa domin tabbatar da cewa muna da man fetur da iskar gas, kuma zan ci gaba da yin hakan ta hanyar ziyartar ƙasashen yankin Gulf domin tabbatar da wadatar kayan makamashinmu."

    Macron zai shafe kwanaki uku a yankin Gulf, bayan ya isa Kuwait da safiyar yau. Daga nan zai ziyarci Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), Bahrain da Qatar kafin ya koma Faransa a ranar Laraba.

  3. Jirgin Austria ya yi saukar gaggawa bayan tashinsa daga Isra'ila

    Rahotannin kafafen yaɗa labaran Isra'ila sun ce wani jirgin saman kamfanin Austrian Airlines ya yi saukar gaggawa a Sofia, babban birnin ƙasar Bulgaria, kimanin sa'a guda bayan tashinsa daga Tel Aviv zuwa Vienna.

    Jaridar Times of Israel ta ruwaito a daren Lahadi (16 ga Oktoba) cewa jirgin ya aika da saƙon neman ɗauki na gaggawa bayan an samu fargaba kan yiwuwar wata barazanar tsaro a lokacin tashin.

    A cewar rahotannin, ganin wani abu da ake zargi a cikin jirgin ne ya haifar da damuwar tsaro.

    Fasinjojin da ke cikin jirgin sun shaida wa kafafen yaɗa labaran Isra'ila cewa an ayyana yanayin gaggawa ne bayan an karɓi wani rahoto daga wanda ba a san ko wanene ba, wanda ya yi ikirarin cewa akwai bam a cikin jirgin.

  4. MDD za ta rage yawan tallafin abincin a Gaza

    Shirin samar da Abinci na Duniya ya ce ƙarancin kudade na tilasta masa rage tallafin da ya ke bai wa mutane a Gaza.

    Adadin mutanen da shirin na Majalisar Dinkin Duniya ke taimakawa a yankin Falasdinawa zai ragu da kusan mutane dubu dari biyar.

    Rage tallafin ya zo ne yayin da hunturu ke karatowa kuma yawancin iyalai - wadanda ke zaune a cikin tantuna na wucin gadi - har yanzu suna fama da rashin isasshen abinci duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka riga aka cimma.

  5. Sallama

    Masu shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wanna rana ta Litinin, mande tushen aiki ko da Nasara na tsaronki kamar yadda Hausa ke yi mata kirari.

    Rabi'atu Kabir Runka ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.