Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya Wannan 31/05/2026

Wannan shafi ne da kawo muku muhimman bayanan dangane da wainar da ake toyawa a Najeriya da sassan duniya na ranar Lahadi 31 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Isra'ila ta yi kutse mai girma a kudancin Lebanon

    Sojojin Isra'ila sun kwace iko da wani yanki a kudancin Lebanon da ke da tsaro, wanda shi ne kutse mafi nisa da Isra'ila ta yi a kasar a cikin shekara 25, lamarin da ya janyo kushe daga Faransa .

    Firamistan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce kwace iko da wajen shakatawar na Beaufort castle - wanda yake kusa da Tekun Litani - babbar nasara ce wajen yaki da Hezbollah.

    Lebanon ta ce hare-haren na Isra'ila ya jikkata ma'aikatan asibiti, sannan ta zargi kasar ta Isra'ila da kai harin da gangan domin lalata muhimman wurare.

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce babu hujjar hare-haren na Isra'ila a kudancin Lebanon, sannan ya bukaci kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya kira taron gaggawa a ranar Litinin.

  2. Tinubu ya tura wakilai jihar Oyo da aka sace ɗalibai

    Shugaba Bola Tinubu ya tura wata babbar tawaga ta gwamnati zuwa ƙauyukan Esiele da Yawota da ke yankin Ogbomoso a Jihar Oyo bayan sace ɗalibai da malamai kusan 46.

    A cewar Jaridar DailyPost, tawagar ta ƙunshi Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro, Nuhu Ribadu, da Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Tunde Disu.

    Sauran mambobin tawagar sun haɗa da Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa; Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe; da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Hulɗa da Jama'a, Sunday Dare.

    Wasu ƴan ta'adda dai sun kai hare-hare lokaci guda a makarantu biyu na Baptist Nursery da Primary School inda suka yi garkuwa da ɗalibai da malamai kusan 46.

    Biyo bayan haka ne Shugaba Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su ɗauki matakan gaggawa tare da haɗa ƙarfi domin ceto waɗanda aka sace da kuma kamo masu laifin.

    Sai dai har zuwa yanzu ba a samu nasarar kuɓutar da su ba.

  3. Ana zaɓen shugaban ƙasa a Colombia

    Al'ummar ƙasar Colombia na kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa wanda zai iya sake fasalta manufofin tsaron ƙasar da kuma dangantakarta da ƙasar Amurka.

    Sai dai yaƙin neman zaɓen da aka gudanar ya zo da tashe-tashen hankula, kuma an tura kusan sojoji da jami'an 'yan sanda 250,000 domin tabbatar da tsaro.

    Shugaban ƙasar mai ra'ayin gurguzu, Gustavo Petro, wanda ba zai iya neman wani wa'adi ba, ya buƙaci jama'a su tabbatar da sahihancin tsarin zaɓen.

    A wani ɓangaren kuma, amininsa, Iván Cepeda, ya ce zai ci gaba da tattaunawa kai tsaye da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya kamar yadda gwamnati ke yi a yanzu.

    Bayan kaɗa ƙuri'arsa a Barranquilla, lauya mai ra'ayin mazan jiya, Aberlardo de la Espriella, ya ce zai ɗauki tsauraran matakan soja domin yaƙi da laifuffuka da fataucin miyagun ƙwayoyi.

  4. Jagoran addini ne alkiblarmu - Majalisar Iran

    A wani sako kafin fara shekara ta uku ta majalisar Iran, shugabanta Mohammad Baqer Qalibaf ya ce sakon jagoran addin Iran ne alkiblar majalisar ta 12.

    Shugaban majalisar ya ce hadin kai tsakanin majalisar da bangaren gwamnati na da matukar muhimmanci wanen cigaban kasar.

    Sai dai ya nanata cewa majalisar na da 'yanci kuma hadin kan ba ya nufin wofantar da 'yancinsu ga bangaren zartarwa.

    Ya kuma ce dole duk ayyukan da majalisar za ta yi su zama domin cigaban al'ummar kasar da ma kasar baki daya.

    A game da yakin da kasar ke ciki, shugaban majalisar ya ce babu amana da yarda tsakaninsu da makiya, inda ya ce, "muna da muradummu da muke som cimmawa. Kuma dole mu same su."

    "Ba za mu amince da wata yarjejeniya ba har sai mun tabbatar an kare muradun 'yan kasarmu," in ji shi.

  5. Ma’aikatan lafiya 13 sun jikkata a harin Isra’ila kusa da asibiti a Lebanon

    Ma’aikatar Lafiyar Lebanon ta sanar da cewa ma’aikatan lafiya 13 sun jikkata sakamakon wani harin sama da Isra’ila ta kai kusa da wani asibiti a birnin Tyre da ke kudancin kasar.

    A cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce harin ya afku ne a kusa da Asibitin Hiram, inda ya haddasa raunuka ga ma’aikatan asibitin tare da jawo babbar illa ga gine-ginen cibiyar lafiyar.

    Sanarwar ta ce, “Isra’ila sun kai hari a kusa da Asibitin Hiram da ke Tyre, lamarin da ya jikkata ma’aikatan asibitin 13 tare da haddasa mummunar barna ga asibitin.”

    Lamarin na faruwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke nuna cewa sojojin Isra’ila na ci gaba da zurfafa kutsawa cikin yankunan Lebanon.

    Ma’aikatar Lafiyar Lebanon ta kuma yi kira ga kasashen duniya da su dauki mataki domin dakile abin da ta kira fadadawa da tsananta hare-haren Isra’ila a kasar.

  6. An kama mutane da dama bayan rikicin murnar nasarar PSG a Faransa

    Akalla mutum 219 ne suka jikkata yayin rikice-rikicen da suka barke tsakanin magoya bayan kwallon kafa da ‘yan sanda a sassan Faransa bayan da PSG ta lashe gasar Champions League bayan doke Arsenal.

    Ministan Harkokin Cikin Gida na Faransa, Laurent Nuñez, ya ce mutane takwas na cikin mawuyacin hali, yayin da jami’an ‘yan sanda 57 suka samu raunuka a lokacin rikicin.

    A cewarsa, an kama mutum 780 bisa zargin hannu a tashin hankalin, kuma fiye da mutum 450 ne suka tsare.

    Haka kuma wani mutum ya mutu bayan wani hatsari da ya afku a kan wata babbar hanya a Paris da masu tarzoma suka yi yunkurin toshe ya da daddare.

    Mahukunta sun tura jami’an tsaro kusan 6,000 domin tabbatar da tsaro yayin faretin murnar nasarar da za a gudanar kusa da Hasumiyar Eiffel a ranar Lahadi.

  7. Kisan fitaccen malamin addini ya haddasa rikici a wata al’umma a jihar Kwara

    An kashe wani fitaccen malamin addinin Musulunci, Alfa Ilyasu, a garin Ilesha-Baruba da ke Karamar Hukumar Baruten a Jihar Kwara, lamarin da ya haifar da tashin hankali a yankin kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Shugabannin al’ummar sun tabbatar da cewa malamin, wanda ake girmamawa sosai a Baruten da makwabtan yankuna, ya rasa ransa ne bayan an kai masa hari da adda a cikin yanayi da har yanzu ake ci gaba da bincike a kai.

    Dan majalisar dokokin Jihar mai wakiltar mazaɓar Okuta/Yashikira, Muhammed Baba Saliu, ya ce har yanzu ana tattara bayanai kan yadda lamarin ya faru.

    Ya ce an riga an binne malamin, sannan rahotanni sun nuna cewa ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da hannu a kisan an kashe shi, an kama wani, yayin da wani kuma ya tsere.

    Tsohon ƙhugaban ƙaramar hukumar Baruten, Abdulrasheed Ibrahim, ya ce bayanan farko sun nuna cewa harin ya faru ne da misalin karfe tara na safe yayin da ake gudanar da karatun Alkur’ani a harabar gidan malamin.

    Ya ce an garzaya da malamin asibiti amma daga bisani ya rasu sakamakon raunukan da ya samu.

    Sarkin Ilesha-Baruba, Halidu Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa shugabannin gargajiya da na addini su yi gaggawar shiga tsakani domin hana rikicin ya kazanta.

    Ya ce har yanzu ba a san takamaiman abin da ya faru tsakanin malamin da wanda ake zargi da kai masa harin ba.

  8. Ba za mu amince da duk wata yarjejeniya ba sai mun tabbatar za a biya mu diyya - Iran

    Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya bayyana cewa Iran ba za su amince da kowace yarjejeniya ba har sai sun tabbatar an kare haƙƙin al’ummar kasar gaba ɗaya.

    A jawabin da ya yi kafin fara zangon shekara ta uku na majalisar, Qalibaf ya ce sakon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci shi ne abun da za su yi amfani da shi yana mai jaddada cewa ba za a dogara da kalmomin makiya ba.

    Ya kuma ce dole ne majalisa ta guji rikice-rikicen da ke lalata aiki, tare da mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, musamman wajen tabbatar da sakamako mai kyau a fili ga jama’a.

    A bangaren dangantakar kasa da kasa, rahotanni daga kafafen yada labarai na Amurka sun ce shugaban Amurka, Donald Trump, ya kara tsaurara sharuɗɗa a sabon daftarin farko na yarjejeniya da Iran, inda aka ce an tura shi zuwa Tehran don nazari.

  9. Makinde ya kai ziyara ga iyalan ɗalibai da malaman da aka sace a Oyo

    Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya tabbatar wa iyalan ɗalibai da malamai da aka sace a Karamar Hukumar Oriire cewa gwamnatinsa na yin duk mai yiwuwa domin ganin an ceto su lafiya.

    Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wata ziyara da ya kai garin Ahoro-Esiele, inda ya gana da iyalan waɗanda abin ya shafa da shugabannin al’umma da mazauna yankin a harabar makarantar L.A. Basic School.

    Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da al’umma ke cikin damuwa da fushi kan sace ɗalibai da malamai da dama, lamarin da ya kara tayar da hankalin jama’a kan tsaron makarantu a jihar.

    A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X, gwamnan ya ce ya saurari korafe-korafen iyalan tare da sake tabbatar musu da cewa gwamnati na aiki ba dare ba rana domin ganin an dawo da waɗanda aka sace gidajensu lafiya.

    Sace ɗaliban ya faru ne a ranar 15 ga Mayu, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari makarantu uku a yankin Esiele, inda suka tafi da dalibai da malamai 45.

    Bayan ‘yan kwanaki, rahotanni sun ce ɗaya daga cikin malaman da aka sace, wanda ake zargin malamin lissafi ne, an kashe shi.

    Lamarin ya jawo matukar allawadai daga jama’a, inda gwamnati da Shugaba Bola Ahmed Tinubu suka yi alkawarin ɗaukar mataki domin kubutar da waɗanda aka sace da kuma hukunta masu laifi.

  10. Faransa ta nemi taron gaggawa na MDD bayan Isra'ila ta karɓe gidan tarihi a Lebanon

    Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Noël Barrot, ya sanar da cewa Faransa ta nemi a kira taron gaggawa na Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya bayan rahoton kwace tsohon katanga mai tarihi na Beaufort da sojojin Isra’ila suka yi a Lebanon.

    Barrot ya bayyana hakan ne a tashar talabijin na BFM, inda ya ce duk da cewa Faransa na amincewa da ‘yancin Isra’ila na kare kanta, babu wani dalili da zai halatta ci gaba da ayyukan soji da fadada shiga cikin yankin Lebanon.

    Ya nuna damuwa kan yadda ake kara faɗaɗa kasancewar sojojin Isra’ila a ƙasar Lebanon, yana mai cewa dole ne Majalisar Tsaro ta duba lamarin cikin gaggawa.

    A gefe guda, Ministan Tsaron Isra’ila ya sanar cewa an karɓe sansanin tarihi da muhimmanci na Shaqif (Beaufort), inda ya ce sojojinsa sun sake komawa wurin bayan shekaru 44 tun daga yakin Lebanon na 1982, sannan suka daga tutar Isra’ila a wurin.

    Wannan katafaren gini mai tarihi yana da mahimmanci a fannin soja saboda yana bai wa mai rike shi damar ganin yawancin kudancin Lebanon, lamarin da ke kara masa muhimmancin dabarun yaki.

  11. An sace tsohon babban jami'in sojin Najeriya da matarsa a Katsina

    An sace tsohon babban jami’in sojan Najeriya kuma tsohon Daraktan Yada Labaran Tsaro, Manjo janar Rabe Abubakar, tare da matarsa a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    Rahotanni sun ce an yi garkuwa da su ne a ranar Asabar yayin da suke kan hanyar zuwa wani bikin aure, inda ‘yan bindiga suka tare motarsu a yankin Matazu.

    Mai magana da yawun sojojin Najeriya, Michael Onoja, ya tabbatar da faruwar lamarin ga BBC a ranar Lahadi, yana mai cewa ana ci gaba da kokarin ceto su tare da bin diddigin wadanda suka sace su.

    Wata majiya ta ce direban motar ya samu nasarar tserewa duk da raunin harbin bindiga da ya samu, yayin da ma’auratan aka tafi da su zuwa cikin dazukan da ke kusa da yankin.

    Lamarin ya sake bayyana matsalar tsaro da ke addabar sassan arewa maso yammacin Najeriya, inda ake yawan samun garkuwa da mutane, satar shanu da hare-hare kan kauyuka daga ‘yan bindiga.

    Jihar Katsina na daga cikin yankunan da suka fi fuskantar wannan matsala a shekarun baya-bayan nan, lamarin da ke ci gaba da janyo damuwa a fadin kasar.

    Wannan hari ya biyo bayan wani hari da aka kai a kauyen Kiliya da ke karamar hukumar Dutsinma, inda aka kashe aƙalla mutane 16 a ranar Juma’a, yayin bukukuwan Sallar Layya.

  12. Na cika kashi 90 cikin 100 na alƙawuran da na wa mutanen Kano - Gwamna Abba

    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cika kusan kashi 90 cikin 100 na alƙawuran da ta yi wa al’ummar jihar cikin shekaru uku a kan mulki.

    Ya yi wannan bayani ne yayin da ya karbi bakuncin Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umaru, wanda ya kai masa ziyarar Sallah a Fadar Gwamnatin Kano a ranar Asabar.

    A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, ya ce gwamnatin Yusuf ta mayar da hankali kan aiwatar da ayyukan raya kasa da manufofi da suka shafi rayuwar al’umma kai tsaye a fannoni daban-daban.

    Ya bayyana cewa an samu ci gaba a fannonin ilimi, lafiya, ababen more rayuwa, noma, samar da ruwa, tallafawa matasa da bunkasa tattalin arziki, tare da cewa duk wadannan na nufin inganta rayuwar jama’a da kuma ciyar da Kano gaba mai dorewa.

    A nasa bangaren, Sarkin Rano ya yaba wa gwamnan bisa abin da ya kira manyan nasarori cikin shekaru uku, inda ya ambaci kammala hanyoyi mai tsawon kilomita biyar a Rano, Kibiya da Bunkure, da kuma ci gaban aikin ruwa na Kaluwaiwai.

  13. Jam’iyyar NDC ta tabbatar da Peter Obi da Kwankwaso a matsayin 'yan takararta

    Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ƙarƙashin jagorancin Sanata Seriake Dickson ta bayyana tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben shekarar 2027.

    An bayyana Obi a matsayin wanda zai yi wa jam’iyyar takara ne a babban taron jam’iyyar da aka gudanar a Abuja ranar Asabar.

    Bayan karbar tutar jam’iyyar, Obi ya sanar da tsohon gwamnan Jihar Kano, Musa Kwankwaso, a matsayin abokin takararsa.

    Fitowar Obi a matsayin dan takarar NDC ya sake bude gasar neman shugabancin kasa tsakanin manyan 'yan siyasa uku.

    Wannan na zuwa ne bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, yayin da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC.

    Atiku da Obi dai da farko sun shiga ADC tare da wasu manyan 'yan adawa a watan Yulin 2025 a wani yunƙuri na hada kan adawa domin ƙalubalantar APC a zaben 2027. Sai daga baya Obi ya fice daga ADC tare da Kwankwaso, inda suka koma NDC.

    Shigowar Obi da Kwankwaso cikin NDC tare da magoya bayansu na kungiyoyin Obidient Movement da Kwankwasiyya Movement ya ƙara wa jam’iyyar ƙarfi a fagen siyasa.

  14. Za a kammala batun gyaran gidajen da yaƙi ya lalata nan da Yuli - Iran

    Mai magana da yawun Gwamnatin Birnin Tehran, Abdul Motahar Mohammadkhani, ya bayyana cewa ana sa ran a kammala dukkan batutuwan da suka shafi sake gina da gyaran gidajen da yaƙin baya-bayan nan ya lalata nan da watan Yuli.

    Ya ce an samu kusan kashi 40 cikin 100 na ci gaba wajen sake gina gidajen da lalacewarsu ta kai ga buƙatar rushe su gaba daya tare da sake ginawa.

    Mohammadkhani ya kuma bayyana cewa gidaje kusan 51,000 ne suka samu matsala sakamakon yaƙin.

    Ya ƙara da cewa aikin gyaran gidajen da suka samu ƙananan lalacewa ya kai kashi 97 cikin 100, kuma ana sa ran za a kammala batutuwan da suka shafe su kafin ƙarshen wannan makon.

    A cewarsa, an dora babban nauyin gudanar da aikin sake gina gidajen da suka lalace a kan Gwamnatin Birnin Tehran.

    Mai magana da yawun ya kuma ce har yanzu ba a sanya takamaiman wa'adin lokacin da iyalan da ke zaune a otal-otal na wucin gadi za su bar wuraren ba.

    Ya bayyana cewa a lokacin da yaƙin ya fi tsanani, iyalai sama da 2,300 ne suka kasance a matsugunan gaggawa, amma yanzu adadin ya ragu zuwa iyalai 1,629.

  15. Iran ta ce ta kakaɓo jirgin yaƙin Amurka ƙirar MQ-1

    Rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da cewa ta harbo wani jirgin yaɓi maras matuki na Amurka ƙirar MQ-1 da ta kai mata hari da shi a safiyar yau

    A cikin wata sanarwa da sashen hulda da jama'a na rundunar ya fitar, ta ce jirgin ya yi yunkurin shiga sararin ruwan Iran domin gudanar da ayyukan da ta bayyana a matsayin na tada hankali, amma an gano shi cikin gaggawa tare da harbo shi ta amfani da makamai masu linzami na zamani na rundunar.

    Rahotannin kafafen yaɗa labaran Iran sun ce rundunar kariyar sararin samaniyar IRGC ta jaddada cewa yankunan ruwan ƙasar na ƙarƙashin cikakken kulawarta, kuma za ta mayar da martani cikin tsanaki ga duk wani yunƙurin keta huruminta.

    Ya zuwa yanzu, rundunar sojojin Amurka (CENTCOM) ba ta fitar da wata sanarwa ko martani kan wannan iƙirari da Iran ta yi ba.

  16. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Lahadidaga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangidda ke fatab sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.