Ƴan bindiga sun kashe babban limami a jihar Sokoto
Ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Kuda-Kuda da ke ƙaramar hukumar Goronyo a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, inda suka kashe babban limamin ƙauyen Liman Audu tare da wasu mutane uku.
Mazauna ƙauyen sun ce baya ga mutane uku da aka kashe Yahaya Hasanu, Zahara Mu'azu da Ibrahim Dayyabu, an kuma yi garkuwa da wasu ƴan garin mutum shida.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:58 na daren jiya Talata, inda maharan suka shafe kusan sa’o’i biyu suna harbe-harbe, tare da sace dabbobi da kuma tilasta wa mazauna ƙauyen tserewa daga garin.
Wani mazaunin ƙauyen ya ce: “Muna salla da dare lokacin da muka fara jin harbi daga ko’ina. Mun tayar da iyalanmu daga bacci muka gudu bayan ƙauye domin tsira da rayukanmu.”
Rahotanni sun ce maharan sun shiga gida-gida suna sace mutane, musamman matan masu aure, yayin da suka kuma kashe wasu bayan sun ki bin su daji.
“Bayan sun kashe limamin, sun ci gaba da harbe wasu matasa da suka ki bin su zuwa daji.”
Mazauna yankin sun ce wannan hari shi ne karo na 11 da aka kai wa ƙauyen.
Sai dai har yanzu babu wata sanarwa daga hukumomin jihar.