Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gasar kofin duniya 2026: Mbappe ya yaga ɓarakar Senegal

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Matakin rukuni
France 3 , Senegal 1 at Full time
Faransa
Senegal
Full time
Hutun rabin lokaci Faransa 0 , Senegal 0

Key Events

Faransa

  • K. MbappéGoal 66 minutes, Goal 90 minutes plus 6
  • B. BarcolaGoal 82 minutes

Senegal

  • I. MbayeGoal 90 minutes plus 5
Ba da ƙwallo a ci
Faransa,M. Olise (66 minutes), A. Rabiot (82 minutes)
Senegal,I. Ndiaye (90 minutes plus 5)

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu tare da taimakon AI

  1. Nan muka kawo karshen shirin

    Da fatan kun ji dadin yadda muka kawo muku wannan wasan kai tsaye da Faransa ta yi nasara a kan Senegal da cin 3-1 a wasan farko a rukuni na tara.

    Za mu kawo muku wasan Ingila da Croatia a gobe Laraba tun daga karfe takwas agogon Nigeria da Niger.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tudun Wada ke muku asuba ta gari.

  2. Wasannin da za a buga ranar Laraba

  3. Yadda Faransa ta mamaye wasan

  4. An tashi wasan

    Faransa ta samu maki uku da kwallo uku a kan Senegal a wasan farko a rukuni na tara, inda Faransa ta doke Senegal 3-1 a wasan farko a cikin rukuni.

  5. GOAL - France 3-1 Senegal, Kylian Mbappe

    Wasan ya kare kenan.

    Daga nesa da gidan Senegal Mbappe ya buga kwallo ta fada ragar Senegal.

    Zagaye na biyun nan bai yi wa Senegal kyau ba, komai ya lalace, sai kwallaye ake zura mata.

  6. GOAL - France 2-1 Senegal, Ibrahim Mbaye

    Senegal ta zare daya ta hannun Mbaye, kuma mai kyau ya samu kwallon ya buga ta kuma fada raga.

  7. , Faransa 2-0 Senegal

    An yi karin minti takwas, tuni dai Faransa ta kammala aiki ta samu maki ukun da take bukata a wasan farko a rukuni na tara.

  8. 'Har ila yau, Man yana kan filin wasa', Faransa 2-0 Senegal

    Har yanzu Sadio Mane yana cikin fili, kuma shekaru sun ja shi ba yaro bane.

    Amma dai akwai kwarewa da gogewa da zarar ya samu dama, sai kaga raga na kadawa.

  9. Senegal ta yi canji, Faransa 2-0 Senegal

    Dan wasan Everton, Idrissa Gueye an maye gurbinsa da Pathe Ciss.

  10. , Faransa 2-0 Senegal

    Faransa yanzu ta mamaye wasan babu wani tashin hankali a tare da ita.

  11. GOAL France 2-0 Senegal, Bradley Barcola

    Kwallo mai kyau da Barcola ya samu ya ci, yana yin gaba da gaba da mai tsaron raga, Mendy sai ya daga kwallon sama ta fada raga.

  12. Senegal ta yi canjin yan wasa, Faransa 1-0 Senegal

    Canjin yan wasa biyu daga Senegal.

    Ismaila Sarr da Lamine Camara sun fita daga wasan, inda Ibrahim Mbaye na PSG da Habib Diarra na Sunderland suka maye gurbinsu.

  13. , France 1-0 Senegal

    Da wannan kwallon da Kylian Mbappé ya zura a raga, ya zama ya yi kan-kan-kan da yawan wanda Olivier Giroud ya ci wa Faransa a tarihi.

    Haka kuma, saura ƙwallo uku tsakani ya tarar da dan wasan, Jamus Miroslav Klose mai 16 a gasar cin kofin duniya jimilla.

  14. Olise ne ke haddasa komai a wasan nan, Faransa 1-0 Senegal

    Tawagar Senegal sun kasa tare Olise, kuma tun farko shi ne yake ta raba kwallaye masu hatsari a karawar.

  15. An je hutun shan ruwa, an kuma koma wasan

    Tuni kuma za a ci gaba da wasan. Watakila Faransa ta rama abin da Senegal ta yi mata a gasar cin kofin duniya a 2002.

  16. GOAL - France 1-0 Senegal, Kylian Mbappe

    Kwallo ce mai kyau da Mbappe ya samu daga wajen Olise a cikin gidan Senegal kuma ko taba ta bai yi ya buga ta fada raga.

  17. , Faransa 0-0 Senegal

    Tun da aka koma zagaye na biyu sai kai kora Faransa take yi tana kuma barar da damarnaki.

  18. , Faransa 0-0 Senegal

    Olise na Faransa ya bayar da kwallo mai kyau tsakanin masu tsaron bayan Senegal, sai dai ta yi yawa Mbappe ya kasa tare ta mai tsaron ragar Senegal ya fito da wuri ya tare ta.

  19. Babu wani laifi an ci gaba da wasan, Faransa 0-0 Senegal

    Alkalin wasa, Alireza Faghani: ya ce babu keta a ci gaba da wasan da har yanzu ba ci.