Har yanzu mahaifiyarmu na hannun masu garkuwa - Ɗiyar Janar Rabe
Yarinyar marigayi Janar Abubakar Rabe, wanda ya rasu a hannun ƴanbindiga ta ce suna cikin tashin hankali mara misaltuwa na abin da ya faru da iyayensu.
Bilkisu Rabe Abubakar ta bayyana cewa an jana'izar mafhaifinsu a jiya Asabar da misalin ƙarfe 6:15 na yamma bayan an yi masa Sallah a Masallacin GRA da ke Katsina.
Sai dai ta ce har yanzu mahaifiyarsu wadda aka sace tare da mahaifinsu har yanzu tana hannun masu garkuwar, har zuwa lokacin haɗa wannan labarin.
Hukumomi dai sun lashi takobin tabbatar da cewa sun ceto ta.
An yi garkuwa da Manjo Janar Rabe Abubakar da matarsa a Jihar Katsina a watan da ya gabata, bayan da 'yan bindiga suka kai hari kan motarsu.
Kwanaki kadan kafin mutuwarsa, an ga bullar wani bidiyonsa a daji da ke nuna shi da wani ciwo a kafarsa ta hagu, to sai dai mahukunta a jihar Katsinan sun ce ya rasu a hannun 'yan fashin dajin ne sakamakon fama da ciwon suga da hawan jini.
A cikin shekarun baya-bayan nan, wasu manyan jami’an soja sun rasa rayukansu sakamakon masu garkuwa da mutanen.