Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 20 ga watan Yuni, 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

  2. Hare-haren Isra'ila sun kashe mutum 10 a Gaza

    Jami'an lafiya a Gaza sun ce aƙalla Falasɗinawa 10 ne suka mutu bayan hare-hare ta sama da na bindiga da Isra'ila ta kai yankin a wasu hare-hare daban-daban.

    Kafar yaɗa labarai ta Aljazeera ta ce an kashe ɗaya daga cikin ƴanjaridarta mai suna Ahmed Wishah a wani harin na daban da aka kai kan wani gida a wani sansanin ƴan gudun hijira a tsakiyar Gaza.

    Rundunar sojin Isra'ila ta yi zargin cewa Mista Wishah mamba ne na ƙungiyar Hamas. Kafar Aljazeera ta musanta zargin.

    Tun da farko wani harin na daban ya kashe mutum huɗu ciki har da wata mata da yara biyu a wani gida a Birnin Gaza.

    Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hari kan mayaƙa masu ɗauke da makamai ne a harin.

    Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a wajen Oktoban bara ta dakatar da munanan hare-hare tsakanin Isra'ila da Hamas, amma duk da haka ma'aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce fiye da Falasɗinawa 1,000 ne Isra'ila ta kashe tun bayan hakan.

  3. Ana ci gaba da ƙidaya ƙuri'a bayan kammala zaɓen gwamnan jihar Ekiti

    Ana ci gaba da ƙidaya ƙuri'a bayan kammala zaɓen gwamnan jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya.

    Rahotonni sun ce al'ummar jihar da dama ne suka fita domin kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen na yau da aka gudanar a faɗin ƙananan hukomomin jihar 16.

    Bayanai sun ce tun da misalin ƙarfe 7 na safe masu kaɗa ƙuri'a suka fita rumfunan zaɓe, kodayake ba a fara zaɓen ba sai da ƙarfe 8:30 a wurare da dama.

    An jibge tarin jami'an tsaro a rumfunan zaɓe da wuraren tattara sakamakon zaɓen domin bayar da tsaro a lokacin zaɓukan da kuma ƙidaya ƙuri'u.

    Ƴantakara fiye da 10 ne suka fafata a zaɓen, ciki har da gwamnan jihar mai ci na jam'iyyar APC da ke neman wa'adin mulki na biyu.

  4. Sojojin Amurka sun ce Iran ba ta da iko da mashigar Hormuz

    Kakakin rundunar sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya US Central Command, Tim Hawkins ya shaida wa kafofin yaɗa labaran Al Jazeera da Washington Post da kuma Reuters cewa ''Iran ba ta da iko da mashigar Hormuz''.

    Da yammcin yau ne dai Iran ta sanar da rufe mashigar, saboda zargin Isra'ila da Amurka da saɓa yarjejeniyar da aka cimma ta kawo ƙarshen yaƙin ɓangarorin biyu, bayan da Iran ɗin ta ta zargi isra'ila da kai hare-hare zuwa Lebanon

    Rahotonni sun ambato shi yana faɗin cewa ''jirage na ci gaba da wucewa ta mashigar'', yayin da ya ce dakarun Amurka na lura da mashigar''.

    BBC ta rundunar Centcom domin ji daga gareta.

  5. Musayar yawu ta turnuƙe tsakanin Trump firaministar Italiya

    Musayar yawu tsakanin Shugaba Trump da firaministar Italiya, Giorgia Meloni ta ci gaba da faɗaɗa, bayan da shugaban Amurka ya jaddada iƙirarinsa cewa Ms Meloni ta roƙe shi su ɗauki hoto tare a taron ƙungiyar ƙasashe masu arziki ta G7 da aka gudanar a baya-bayan nan.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump ya yi iƙirarin cewa shugabar Italiyar ''ba ta yi daidai da matakin shahararta ba''.

    A nata ɓangare Ms Meloni ta mayar da martani, cikin wani saƙo da ta wallafa tana mai cewa shahararta ba damuwar Trump ba ce - don haka ya mayar da hankali ga tasa shaharar.

    A baya dai shugabannin biyu masu tsattsauran ra'ayi sun kasance manyan abokai, to sai dai dangantar tasu ta yi tsami bayan da aka bayar da rahoton cewa Italiya ta hana sojojin Amurka damar amfani da sansaninta da ke Sicily don kai hare-hare zuwa cikin Iran.

  6. Iran ta gargaɗi jiragen ruwa kada ku kusanci mashigar Hormuz

    Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta sanar da rufe mashigar Hormuz ga dukkan jiragen ruwa, tare da gargadin cewa kada su kusanci yankin.

    Ta zargi Amurka da Isra’ila da karya yarjejeniyar tsagaita wuta, abin da ya kara dagula yanayin tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙaruwar tashin hankali a yankin, musamman bayan zargin ci gaba da kai hare-hare duk da yarjejeniyar dakatar da faɗa.

    Rundunar ta ce matakin da ta dauka ya biyo bayan abin da ta kira saɓawa yarjejeniyar da aka kulla domin kawo karshen rikici.

    IRGC ta nuna damuwa kan hare-haren da ake zargin Isra’ila na kai wa a kudancin Lebanon, tana mai cewa hakan na daga cikin manyan dalilan da suka sa aka rufe mashigin.

    Ta ce wannan na nuna rashin cika alkawuran da aka dauka a yarjejeniyar tsagaita wuta.

    A wani bangare, rundunar ta fitar da kakkausar gargadi ga dukkan jiragen ruwa, tana mai cewa duk wanda ya kuskura ya kusanci mashigar zai iya jefa kansa cikin hadari.

  7. Iran ta yi barazanar rufe mashigar Hormuz saboda zargin saɓa yarjejeniya

    Hedkwatar juyin juya halin Iran ta Khatam al-Anbiya ta sanar da cewa za a rufe mashigar Hormuz ga dukkan jiragen ruwa, a matsayin mataki na farko na mayar da martani ga abin da ta kira karya alkawari da Amurka da kawayenta suka yi.

    Wannan sanarwa ta fito ne a wata sanarwa da aka fitar, inda aka ce an dauki matakin ne sakamakon sabawa yarjejeniyar da aka kulla domin kawo karshen yaki.

    Sanarwar ta zargi Amurka da karya sharadin farko na yarjejeniyar, wanda ya tanadi kawo karshen dukkan ayyukan soji a dukkan fannoni, ciki har da kasar Lebanon.

    Haka kuma ta zargi Isra’ila da ci gaba da karya yarjejeniyar a kudancin Lebanon, inda aka ce hare-haren sun janyo mutuwar mutane da dama tare da tilasta wa dubban jama’a ƙauracewa gidajensu.

    Bugu da kari, ta bayyana rashin janyewar sojojin Isra’ila daga kudancin Lebanon a matsayin daya daga cikin manyan dalilan ɗaukar wannan mataki.

    A cewar su, waɗannan abubuwa na nuna rashin cika alkawuran da aka dauka a karkashin yarjejeniyar da aka kulla tsakanin bangarorin.

    Khatam al-Anbiya ta jaddada cewa rufe mashigiar Hormuz shi ne mataki na farko tana mai gargaɗin cewa za a ɗauki karin matakai idan har aka ci gaba da karya yarjejeniyar.

  8. Gwamnatin Bauchi ta rufe masallaci saboda rikicin liman da ƴan kwamati

    Gwamnatin Jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya ta rufe Masallacin Ibadurrahman da ke unguwar Shingen Abba a cikin garin Bauchi, sakamakon rikicin da ya shafe kusan shekaru uku yana gudana tsakanin kwamitin gudanarwar masallacin da limaminsa.

    Matakin ya zo ne domin daƙile yiwuwar ɓarkewar rikici da ka iya janyo asarar rayuka a tsakanin al’umma.

    Kwamishinan Hisba na Hukumar Shari’ar Musulunci ta jihar, Barrista Aminu Balarabe Isah, ya bayyana wa manema labarai cewa an ɗauki wannan mataki ne bisa umarnin gwamnatin jihar tare da sahalewar kotu.

    Ya ce rikicin ya daɗe yana faruwa kuma ya kai kotuna daban-daban, amma har yanzu ɓangarorin sun kasa cimma matsaya.

    A cewarsa, an taɓa kai batun gaban Hukumar Shari’ar Musulunci tun shekarar 2023 inda aka yi ƙoƙarin sulhu tare da shimfiɗa dokokin zaman lafiya, amma hakan bai haifar da sakamako ba.

    Ya ƙara da cewa ko da aka taɓa cire limamin masallacin na wani lokaci domin a shawo kan rikicin, bayan an dawo da shi, sai matsalar ta sake ɓarkewa.

    Barrister Aminu ya jaddada cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani rikici da zai iya jefa rayukan jama’a cikin haɗari ba.

    "Dokar ƙasa ta bai wa kowa dama ya yi addininsa, amma idan za a samu rashin zaman lafiya da zai kawo rikici ko rasa rai, to ba za a saka ido ba. Wannan dokar muka yi amfani da ita domin kare lafiyar al'umma muka zo muka rufe wannan Masallaci.

    Ya kuma gargaɗi al’ummar yankin su bi doka, yana mai cewa duk wanda ya karya umarnin rufe masallacin zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada, har sai an samu maslahar warware rikicin.

  9. Iran ta kama mutum uku da zargin hannunsu a zanga-zangar watan Janairun bara

    Ma’aikatar leken asirin Iran ta sanar da kama mutane uku a lardin Ilam da ake zargi da hannu a zanga-zangar watan Janairun bara.

    Hukumar ta ce ana tuhumar mutanen da jagoranci zanga-zanga, kone-kone da lalata dukiyar jama’a, da kuma amfani da makamai.

    Haka kuma ta ce an kama wasu ƙarin mutane 14 da ake zargin suna cikin wata kungiyar “lalata tsaro a tituna” wadda ke aiwatar da umarnin makiya a lokacin yakin.

    A wani ɓangare kuma, babban alƙalin lardin Azerbaijan ta Yamma, Nasser Atabati, ya bayyana cewa akalla mutane 480 ne aka kama tun bayan fara hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran.

    Ya kara da cewa an yanke hukunci kan wasu mutum 10 da ake zargi da yi wa hukumar leken asirin Isra’ila, Mossad, aiki.

    Waɗannan kamun suna zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyoyin kare hakkin dan Adam ke cewa an ƙara tsaurara matakan danniya kan masu adawa da gwamnati a Iran.

    Ƙungiyar Amnesty International ta ce sama da mutane 6,000 ne aka kama ba bisa ƙa’ida ba tun bayan fara yakin, yayin da aka kashe akalla mutane da dama ta hanyar hukuncin kisa.

    A lokaci guda, kwararrun Majalisar Dinkin Duniya sun yi gargadi cewa duk wata yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka da ba ta yi la’akari da halin da ake ciki na hakkin bil’adama a Iran ba, ba za ta zama cikakkiya ba.

  10. An ci gaba da kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamnan Ekiti

    Bayan shafe shekaru hudu, al’ummar jihar Ekiti da ke yankin Kudu maso Yammacin Najeriya sun koma rumfunan zabe domin zaɓen sabon gwamnan da zai jagorance su na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

    Masu kada kuri’a sun fara tururuwa zuwa rumfunan zabe domin kaɗa ƙuri'arsu.

    Rahotanni sun nuna cewa kimanin ‘yan takara 14 ne ke fafatawa a wannan zaɓe, ciki har da gwamna mai ci Biodun Oyebanji wanda ke neman wa’adi na biyu.

    Haka kuma an bayyana cewa huɗu daga cikin ‘yan takarar suna da mata a matsayin mataimakansu, abin da ke nuna ƙarin shiga mata a harkokin siyasa.

    An fara kada kuri’a ne da misalin karfe 8:30 na safe, kuma ana sa ran za a rufe rumfunan zabe da karfe 2:30 na rana, yayin da fiye da mutane miliyan daya ake sa ran za su kada kuri’unsu a rumfunan zabe guda 2,445 da ke fadin jihar.

    Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta tabbatar da cewa ta shirya tsaf domin gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci, tare da rarraba kayan aiki a kan lokaci.

    Haka kuma jami’an tsaro sun bazu a dukkan fadin jihar domin tabbatar da zaman lafiya da gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

  11. A hankali za a saki kadarorin ƙasarmu da aka ƙwace gaba ɗaya - Iran

    Mataimakin shugaban kula da harkokin zartarwa a Iran, Mohammad Jafar Ghaempanah, ya bayyana cewa za a saki kadarorin Iran da aka ƙwace gaba ɗaya amma a hankali, bisa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da Amurka.

    Ya ce ana sa ran jimillar kudaden za su kai kusan dala biliyan 25, kuma za a saki su ne a matakai daban-daban.

    A wata hira da ya yi da kafar labarai ta IRNA, Ghaempanah ya ce tafiyar da shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya yi zuwa Qatar tare da tawagar tattaunawa, ta mayar da hankali ne kan yadda da kuma tsarin da za a bi wajen sakin kuɗaɗen.

    Ya kuma bayyana cewa rage barazanar yaƙi a ƙasar zai taimaka wajen sauƙaƙa wasu matsin tattalin arziki ga al’umma.

    Haka kuma, ya ce kudaden da za a saki za su kasance an tanade su ne domin bunkasa manyan ayyukan more rayuwa kamar hanyoyi, tituna da filayen jiragen sama domin inganta rayuwar jama’a.

    A ɓangaren Amurka kuwa, shugaban kasa Donald Trump ya taɓa bayyana cewa wadannan kudade na Iran ne kuma ya kamata a mayar musu da su, sai dai a lokaci guda ya musanta cewa Amurka za ta biya Iran wata kudi kai tsaye, yana mai jaddada cewa babu wani kaso na dala biliyan 300 da Amurka za ta bayar, illa dai yiwuwar wasu kasashe su zuba jari idan Iran ta bi sharuddan yarjejeniyar.

  12. Fararen hula bakwai sun mutu a fashewar bam a Pakistan

    Rahotanni daga arewa maso yammacin Pakistan sun ce fashewar bama-bamai biyu a gefen hanya sun kashe akalla fararen hula bakwai a lardin Khyber Pakhtunkhwa.

    ‘Yan sanda sun bayyana cewa fashewar farko ta afkawa wata mota mai zaman kanta da ke dauke da fasinjoji, inda ta hallaka mutum biyar nan take.

    Ba da jimawa ba bayan haka, wata fashewar ta biyu ta auku a wurin, inda ta nufi mutanen da ke kokarin kai wadanda suka jikkata asibiti, tare da kashe karin mutum biyu.

    Har yanzu babu wata kungiyar da ta dauki alhakin hare-haren, duk da cewa kungiyar Tehreek-e-Taliban Pakistan na da karfi a yankin. Pakistan dai ta sha zargin Afghanistan da bai wa ‘yan ta’adda mafaka a kan iyakar kasashen biyu inda suke kai irin wadannan hare-hare.

  13. 'Ƴan jarida za su fara yi wa sojoji rakiya wajen ayyukan tsaro'

    Gwamnatin Najeriya na nazarin wani sabon tsari da zai saka 'yan jarida yi wa sojoji rakiya yayin wasu zaɓaɓɓun ayyukan tsaro kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

    An ce wannan mataki na da nufin inganta yadda ake ruwaito harkokin tsaro tare da bai wa jama’a damar fahimtar ainihin abin da ke faruwa a fagen yaki da ta’addanci da sauran barazanar cikin gida.

    Ministan tsaro, Janar Christopher Musa, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wani taron tsaro na kasa da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) ta shirya a Abuja.

    Ya ce wannan tsari zai kara dankon zumunci tsakanin kafafen yada labarai da hukumomin tsaro tare da karfafa gaskiya da fahimta a ayyukan soji.

    Ya kara da cewa rawar da kafafen yada labarai ke takawa ba karama ba ce wajen gina fahimtar jama’a game da harkokin tsaro da tabbatar da zaman lafiya a kasa.

    A cewarsa, a wannan zamani, yaki ba wai kawai a filin daga ake gwabzawa ba, har ma yana da nasaba da bayanai da labaran da ake yadawa, wanda ke sanya ‘yan jarida zama muhimman abokan hulda a tsarin tsaron kasa.

    Ministan ya jaddada cewa nasarar ayyukan tsaro ba wai kawai auna ta ne da nasarorin soji ba, har ma da yadda jama’a ke da yarda da hukumomin tsaro.

    Ya kara da cewa ingantacciyar hadin gwiwa tsakanin ‘yan jarida da jami’an tsaro za ta taimaka wajen kawar da yada jita-jita, sabani a rahotanni, da kuma kara amincewar jama’a yayin da Najeriya ke fuskantar kalubalen tsaro daban-daban.

  14. Cimma yarjejeniya da Iran ta ceci tattalin arziƙin duniya – Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya kare sabon yarjejeniyar da aka cimma da Iran, yana mai cewa ta ceci duniya daga fadawa cikin matsananciyar koma bayan tattalin arziki.

    A wata hira da shafin labarai na Axios, Trump ya bayyana cewa rikicin da ke tsakanin bangarorin ka iya haddasa “durkushewar tattalin arziki ta duniya,” amma yarjejeniyar da suka kulla ta dakatar da hakan.

    Trump ya ce yarjejeniyar da aka cimma na daga cikin abubuwan da za su iya jefa tattalin arzikin duniya cikin hadari idan ba a shawo kansu ba.

    A cewarsa, matakin da ya dauka ya taimaka matuka wajen kauce wa irin wannan matsala, yana mai jaddada muhimmancin yarjejeniyar wajen samar da kwanciyar hankali a tattalin arziki.

    A wata fuska ta daban, Trump bai kawar da yiwuwar daukar irin wannan mataki kan kasar Cuba ba, yana mai cewa hakan “na iya yiwuwa.” Ya kuma sake kare matakinsa na janyewa daga yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015, yana mai cewa da ba a soke yarjejeniyar ba, da Isra’ila ba za ta wanzu ba a yau..

  15. Ministan harkokin wajen Iran zai tafi Switzerland domin shiga tattaunawar zaman lafiya da Amurka

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, na shirin tafiya zuwa ƙasar Switzerland a ranar Asabar domin shiga tattaunawar zaman lafiya da Amurka, kodayake har yanzu ba a tabbatar da jadawalin tafiyar ba kuma ana iya samun sauyi.

    Rahoton Axios ya nuna cewa Araqchi ya bayyana wa wasu jakadun ƙasashe masu shiga tsakani cewa tsagaita wuta a Lebanon shi ne muhimmin abin da zai ƙayyade ko tattaunawar Iran da Amurka za ta ci gaba ko a’a.

    A lokaci guda, wakilin Fadar White House Steve Witkoff na kan hanyarsa ta zuwa Switzerland, yayin da Jared Kushner, wani babban jami’in gwamnatin Amurka, ya riga ya isa ƙasar.

    Ana sa ran fara zagaye na farko na tattaunawar a yankin Bürgenstock, duk da cewa ba a bayyana takamaiman ranar farawa ba.

    Rahotanni sun kuma nuna cewa sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, zai ziyarci Gabas ta Tsakiya nan gaba kadan domin ƙara ƙoƙarin diflomasiyya.

    Iran ta jaddada cewa dole ne a tabbatar da tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hezbollah na Lebanon kafin ta shiga tattaunawar, inda majiyoyi suka ce hakan shi ne sharadin ci gaba da shirin zaman lafiya.

  16. Isra’ila ta kashe mutum biyar a hare-hare a Lebanon duk da amincewa da tsagaita wuta

    Akalla mutum biyar sun mutu a sabbin hare-haren sama da Isra’ila ta kai a kudancin Lebanon, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka sanar da ita tsakanin Isra’ila da kungiyar Hezbollah.

    Hare-haren sun faru ne a yankin Nabatiyeh, inda jiragen yaki da makamai masu linzami suka lalata gidajen fararen hula.

    Rahotanni sun ce an ci gaba da harba bindigogi da manyan makamai a yankin, abin da ke kara nuna irin raunin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma bayan takun-saka mai tsanani.

    Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin ci gaba da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran a kasar Switzerland, wadda sabbin rigingimun Lebanon ke barazana ga nasararta.

  17. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa barkanmu da ganin safiyar yau Asabar.

    Kamar kullum, a yau ma za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya a wannan shafin namu na BBC Hausa kai tsaye.

    Aisha Bbabangida ke fatan kasancewa da ku a wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na Facebook da X da kuma Whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.