Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Adire: Tufafin da ake haɗawa da "buhun fulawa" a shekarun baya
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Iye adire, re, re, iye adire yaro!
Wannan baitin na cikin fitattun baitocin waƙa da suka yi tashe a tsakankanin shekarar 2000, musamman a tsakanin matasa.
A wani fim din Hausa mai suna "Asali" jarumai Aminu Mirror, wanda yanzu aka fi sani da Malam Zaidu ya hau waƙar ta "Iye Adire yaro."
Waƙa ce da Ghalin Money ya rubuta, sannan Sadi Sidi Sharifai da Rabi Muhammad suka rera.
Sai dai tsohuwar waƙa ce suka sabunta, domin waƙa ce da ta kasance tamkar waƙar gaɗa a tsakanin ƴan matan shekarun baya.
Adire ya dawo bakunan mutane ne bayan ministan matasan Najeriya, Ayodele Olawande ya bayyana a ganawarsa da tashar Channels cewa za a sauya kayan masu yi wa ƙasa hidima wato NYSC, sannan ya ambaci tufafin Adire.
Sai dai daga bisani ministan ya ce ba a riga an ƙarƙare kayan da masu hidimar ƙasar za su saka ba, inda ya ce Adire misali ne kawai ya bayar.
''Yaɗin da ake haɗawa da buhun fulawa a zamanin baya''
Game da tarihi da tasirin kayan a zamanin baya, Hajiya Ladi Ladan ta ce kaya ne ne ado da ƙwalisa a shekarun baya.
Dattijuwar wadda ta kai shekara 90 a yanzu, ta ce a lokacin da suke 'yan mata, suna kiran yadin da suna "ɗan buratsotso."
"Adire asali da buhun fulawa ake yi. Ka san da can fulawa da gishiri duk buhunansu na yadi ne. Idan an gama amfani da fulawar, sai a ɗinka buhun ana sakawa. To yaɗin buhun ne ake zuwa a rina. Idan an rina ɗin ne aka kiransa Adire," in ji ta.
Ta ce asali daga yankin Yarbawa tufafin ya fito, amma ya yi tashe sosai a yankin arewacin Najeriya.
"Za ka ga sun ƙuƙƙulle shi, sai a tsoma a cikin rink. Da an buɗe sai ka ga ya yi kala daban-daban. Wannan shi ne Adire."
Sai dai ta ce ba da buhunan kawai ake yi, domin a cewarta, daga baya ana zuwa kamfanin masaƙa, idan sun samu matsala wajen aiki, sai mutane su saya farin kayan su rina shi ya zama Adire.
"Daga baya kuma mutanen Kurmi sun yi na saƙa, wanda ake zama a saƙa, sannan a rina. Har aka fara zuwa da shi arewacin Najeriya, amma yana da tsada sai wane da wane," in ji Hajiya Ladi, wadda ta ƙara da cewa, "duka na yi amfani da su. Da na saƙar da buhun."
Tarihin yadin Adire
A tsawon shekaru da dama, Adire ya kasance ɗaya daga cikin fitattun tufafin gargajiya da suka yi fice a Najeriya.
Kafar Adire world ta ruwaito cewa tarihin Adire na komawa ne zuwa aƙalla ƙarni na 19, duk da ana cewa ganin dabarar rini ta wuce lokacin.
Yadin, wanda ya samo asali daga al'ummar Yarbawa da ke kudu maso yammacin ƙasar, ya kasance hanyar bayyana al'ada, fasaha da kuma samar da kuma samar da sana'a domin dogaro da kai.
Masana tarihi sun bayyana cewa kalmar Adire ta samo asali ne daga kalmomin Yarbanci guda biyu: "adi", ma'ana naɗewa, da "re", wato rini. Saboda haka, Adire na nufin "naɗewa da rini," wato hanyar da ake amfani da ita wajen háɗa yadin.
A cikin shekarun da suka biyo baya ne sana'ar ta bunƙasa, musamman a garin Abeokuta na jihar Ogun a yanzu, da su Ibadan da Osogbo da sauransu.
Yadda ake sana'anta Adire
Kafar ta Adire ta ce a farkon lokacin bunƙasar Adire, mata ne suka fi gudanar da sana'ar. Suna koyon dabarun ne kuma daga iyayensu da kakanninsu, lamarin da ya taimaka wajen adana fasahar gargajiya tare da mayar da ita wata hanyar samun kuɗaɗen shiga.
A yayin sana'anta Adire, ana naɗe yadi, a ɗaure shi ko a ɗinke shi, ko kuma a yi zane da starching garin rogo kafin a tsoma shi a cikin rinin indigo. Bayan an gama rini sai a wanke yadin, shi ne sai sassan da ba a rina ba su kasance fari.
Masana al'adu sun ce zane-zanen Adire ɗauke da ma'anoni da suka shafi rayuwar al'ummar Yarbawa.
Nau'ukan Adire
Daga cikin sanannun nau'ukan Adire akwai kamar yadda kafar ta ruwaito sun haɗa da:
- Alabere: Wanda ake samar da shi ta hanyar ɗinke yadi kafin a yi masa rini.
- Eleko: Wanda ake amfani da starching garin rogo wajen zane-zane kafin rini.
- Olokun: Wanda ya samo sunansa daga alamar ruwa da arziki a al'adun Yarbawa.
Har yanzu ana amfani da yadin Adire wajen ɗinki na zamani, duk da cewa komawa baya a harkokin masana'antu a Najeriya da shigowa da kayayyakin ƙasahen waje ciki har da yaduka ya mayar da harkar baya.